Bikin Ista: Ku yi addu’ar dawowar zaman lafiya, Atiku ga yan Najeriya
- Alhaji Atiku Abubakar ‘yan Najeriya da su yi amfani da bikin Ista wajen yin addu'ar dawowar zaman lafiya a kasar
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bukaci al'umman kasar da su ci gaba da bin ka'idojin kare kai daga korona don bata tafi ba
- Atiku ya kuma jinjinawa ma'aikatan lafiya a kan yadda suka sadaukar da kansu don kare kasar
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da bikin Ista don yin addu’a ga hadin kan Najeriya da kuma dawowar zaman lafiya a kasar.
A sakonsa na Ista ga 'yan Najeriya, Atiku ya tuno da yadda kwayar cutar Coronavirus ta gurgunta harkoki sosai a yawancin kasashen duniya a shekara guda da ta gabata.
Har ila yau tsohon Mataimakin Shugaban kasar, ya jinjina wa ma’aikatan lafiya wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen yaƙi da cutar.
Da yake gargadin cewa kwayar cutar har yanzu tana da karfi sosai, ya bukaci mutane da su ci gaba da bin ka'idoji don kiyaye kansu, jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Bayan ya yi allurar rigakafi: Shugaban kasar Argentina ya kamu da korona
Atiku ya ce, “Bikin Ista na wannan shekara yana da mahimmanci domin shi ne babban bikin kasa na farko da za mu gani bayan fara gudanar da allurar rigakafin cutar Korona.
“Na tuna cewa a lokacin bikin shekarar da ta gabata akwai dokar kulle a duniya kamar yadda akasarin kasashen duniya suka bukaci‘ yan kasa su kasance a gida kuma, a karon farko a cikin tsararraki da yawa, mun yi bikin Ista a cikin wani salo mai sauki.
“Amma labarin bana ya dan bambanta. Yanzu, akwai ingantattun alluran rigakafi da yawa kuma Najeriya ta yi wa kusan mutum miliyan ɗaya daga cikin al’ummanmu allurar rigakafin farko, ta shiga cikin ƙungiyar ƙasashe waɗanda ke yakar cutar.
“Abu na biyu, dole ne mu godewa ma’aikatan lafiyarmu, wadanda suka sadaukar da lokutansu da rayukansu domin mu kai inda muka a yau wajen yaki da mummunar annobar.
“Manufar bikin Ista ba wai don yin biki bane kawai. Lokaci ne da wanzar da soyayya da sadaukarwa."
KU KARANTA KUMA: Hotunan amaryar da tayi biki ba tare da kwaliyya ba ya haddasa cece-kuce
A gefe guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya sake nanata matsayinsa cewa ’yan Najeriya sun fi kyau kuma sun fi karfi a matsayin kasa daya.
Saboda haka ya yi kira ga ‘yan kasar da kar su bari masu barna su raba kasar.
Matsayin Buhari na kunshe ne a cikin sakonsa na bikin Ista wanda mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Femi Adesina ya gabatar wa manema labarai.
Asali: Legit.ng