Buhari ya nuna bakin ciki yayinda yake juyayin rashin kakakin Afenifere Yinka Odumakin
- Shugaba Buhari ya roki Allah da ya sanyaya zukatan dukkanin wadanda ke juyayin mutuwar Yinka Odumakin
- A sakon ta’aziyar sa, shugaban kasar ya ce mai fafutuka yana da sauran abubuwan da zai taimaka wa al’umma
- Har zuwa rasuwarsa, Odumakin ya kasance mai sukar gwamnatin All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa dangi da abokan Yinka Odumakin, sakataren yada labarai na kungiyar Yarbawa, Afenifere kan rashi da suka yi.
Kakakin na Afenifere ya mutu ne a ranar Asabar, 3 ga Afrilu, a sashen kulawa na musamman na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (LASUTH) inda ya ke jinya kan lamuran da suka shafi numfashi saboda matsalar COVID-19.
KU KARANTA KUMA: Bikin Ista: Ku yi addu’ar dawowar zaman lafiya, Atiku ga yan Najeriya
Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa da mataimakansa, Femi Adesina ya fitar, ya nuna alhinin rasuwar dan rajin kare hakkin dan adam din, wanda a cewarsa har yanzu yana da sauran gudummawa ga kasa baki daya.
Wani ɓangare na bayanin da aka wallafa a shafin Facebook ya ce:
"Odumakin ya kuma kasance mai magana da yawun Janar Buhari na wancan lokacin a 2011, lokacin da ya tsaya takarar Shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC), wanda yanzu aka rushe."
Shugaban kasar ya yi addu'a ga Allah, a kan ya ji kan marigayin ya sa ya huta. Ya kuma yi addu'ar Allah ya sanya dangana a zukatan dukkanin wadanda ke juyayin mutuwar dan gwagwarmayar.
KU KARANTA KUMA: Bayan ya yi allurar rigakafi: Shugaban kasar Argentina ya kamu da korona
A gefe guda, mun dai ji cewa kakakin kungiyar kare hakkin Yarabawa, Afenifere, Yinka Odumakin, ya mutu.
Odumakin ya mutu ne a asibitin koyarwan jami'ar jihar Legas bayan gajeruwar rashin lafiya.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Odumakin ya mutu bayan kamuwa da cutar Korona.
Asali: Legit.ng