An kuma: Gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar katakon Oko Baba na jihar Legas
- Hukumar kashe gobara a jihar Legas ta sanar da konewar kasuwar katakon Oko Baba na jihar
- An samu nasarar kashe wutar, sai dai ta yi sanadiyyar konewar kayayyakin aiki da dama
- Babu rahoton mutuwa ko rauni, kuma hukumar na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin
Hukumar kashe gobara da agaji ta jihar Legas ta kashe wutar da ta kama kasuwar katakon Oko Baba dake Ebute Metta a ranar Alhamis, 1 ga watan Afrilu, 2021.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kokarin da ‘yan kwana-kwana suka yi ya hana wutar cillawa zuwa wasu yankunan da ke kusa da wurin.
Mukaddashiyar kwanturola na hukumar kashe gobara da agaji ta Jihar Legas, Misis Margaret Adeseye ce ta bayyana hakan yayin da take yi wa manema labarai bayani game da lamarin.
KU KARANTA: Hukumar zabe ta INEC ta sanar da ranar ci gaba da rajistar katin zabe
A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar,
“Adeseye ta bayyana cewa hukumar ta samu labari da misalin 2:39 na dare wanda ke sanar da cewa kasuwar katakon Oko Baba na ci da wuta kuma nan take aka dauki mataki tare da tura motocin kashe gobara uku da ma’aikata don magance lamarin."
"Ta ci gaba da bayanin cewa da isarsu wurin, sai aka gano cewa gobarar da ta tashi a kasuwar ta kama wurare tana ci kuma ta cinye kayan aiki daban-daban da ake amfani da su wajen yanka, gyarawa da kwalliya ga itace da katako, da kuma sauran kayayyakin aiki.
"Shugabar hukumar kashe gobarar ta ci gaba da bayanin cewa har yanzu ba a san musabbabin lamarin ba saboda jita-jita na cewa da yiwuwar yin sakaci, yayin da aka fara bincike kan musabbabin lamarin.
"Wutar da aka yi ta fama da ita a cikin dare an kashe ta da misaln karfe 7:58 na safe."
KU KARANTA: Shehu Sani: Yajin aikin likitoci ba fa na direbobin tanka bane, a dai duba
A wani labarin, An samu firgici lokacin da 'yan kwana-kwana uku da wasu mazauna gari suka samu raunuka sakamakon wata gobara da ta tashi a jihar Kaduna.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na safe a yankin Bushara da ke kan babbar hanyar Nnamdi Azikwe ranar Talata a wani garejin tanka da ke kusa.
An samu labarin cewa wutar ta dauki tsawon awanni uku kafin daga karshe jami’an hukumar kashe gobara ta jihar suka kashe ta.
Asali: Legit.ng