Shehu Sani: Yajin aikin likitoci ba fa na direbobin tanka bane, a dai duba

Shehu Sani: Yajin aikin likitoci ba fa na direbobin tanka bane, a dai duba

- Bayan shiga yajin aikin likitoci a Najeriya, Shehu Sani ya kirayi gwamnati ta duba lamarin

- Ya ja hankalin gwamnatin tarayya zuwa ga hatsarin da yajin aikin kan iya haifarwa nan gaba

- Hakazalika ya roki gwamnatin da ta gaggauta sauraran bukatun likitocin don ceto rayuka

Biyo bayan tsundumawar kungiyar likitoci na Najeriya yajin aikin sai Baba ya gani, Sanata Shehu Sani ya yi tsokaci mai cike da darasi.

Shehu Sani ya kirayi gwamnatin tarayya da ta duba yarjejeniyar dake tsakaninta da kungiyar likitocin don shawo kan yajin aikin da suka shiga.

Legit.ng Hausa ta gano gargadin Shehu Sani kan lamarin na kiwon lafiya cewa ba lamari ne na wasa ba, yana mai rokon ya kamata gwamnati ta fahimci hatsarin dake tattare da yajin aikin.

KU KARANTA: APC a Ingila: Kanzon kuregene, ba a yi zanga-zangar adawa da Buhari a kasar Landan ba

Shehu Sani: Yajin aikin likitoci ba fa na dibobin tanka bane, a dai duba
Shehu Sani: Yajin aikin likitoci ba fa na dibobin tanka bane, a dai duba Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Hakazalika ya ce shi fa yajin aikin likitoci ba irin na direbobin tanka bane, a cewarsa lamari ne na rayuwa da mutuwa, dan haka a dauki mataki don ceto rayuka.

Ya wallafa a shafinsa na Tuwita a ranar Alhamis cewa:

"Yajin aikin likitoci ba na direbobin Tanka bane. Ya kan zo da mummunan sakamako na rayuwa da mutuwa.
"Baya ga yin allurar rigakafi, ba mu koyi darussa daga annoba don sake fasalin tsarin kula da kiwon lafiyarmu ba. Ya kamata a cika yarjejeniyar NARD don ceton rayuka."

A yau ne kungiyar likitocin Najeriya ta tsunduma yajin aiki bayan bada gargadi da ta yi na tsawon kwanaki amma gwamnati bata saurare ta ba.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun afkawa gidan tsohon ministan wasanni a Filato

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya tana tsara kashe Naira biliyan 396 don yin allurar rigakafin Korona a shekarar 2021 da 2022, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ministar Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Laraba bayan taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta Tarayya, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Zainab ta bayyana cewa wannan adadi na iya raguwa matuka kasancewar Gwamnatin Tarayya na karbar karin gudummawar allurar rigakafin daga kamfanoni masu zaman kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel