Barayi sun afka gidan jarumin Kannywood, sun yi awon gaba da sabuwar motarsa da wasu muhimman kayayyaki
- Barayi sun kai farmaki gidan wani jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nasiru Bello Sani
- Yan bindigar sun kuma sace sabuwar motar da ya saya kirar SUV da sauran kayayyaki masu daraja
- Jarumin wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya yi godiya ga Allah kasancewar basu taba kowa ba
Wasu barayi dauke da muggan makamai sun shiga gidan wani fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Nasiru Bello Sani, wanda aka fi sani da Nasiru Naba da misalin karfe 1:00 zuwa 2:00 na safiyar Laraba.
Sun kuma yi awon gaba da sabuwar motar da ya saya kirar SUV da sauran kayayyaki masu daraja.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An damke sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki a kasar Nijar
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Naba ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa barayin, wadanda ke dauke da bindigogi, sun shiga gidansa da ke Maidile a cikin garin Kano ta karfin tuwo.
Sannan suka tafi da sabuwar motarsa mai kwana daya, da kayayyakinsa masu muhimmanci, da dai sauransu.
“Na karbi motar ne a ranar da ta gabata.
“Lambarta ma ba ta iso ba.
“Godiya ta tabbata ga Allah, ba su cutar da kowa ba. Kawai dai sun dauke motar da muhimman kayayyaki,” in ji shi.
Jarumin ya ci gaba da bayanin cewa tuni daga ya kai rahoton lamarin ga hukumomin da ya kamata sannan kuma ya bukaci magoya bayansa da su saka shi a cikin addu'o'insu.
KU KARANTA KUMA: Kyawawan hotunan ma’auratan da suka raya sunnah watanni 8 bayan haduwarsu a Twitter
A gefe guda, mun ji cewa akalla mutane takwas ne suka mutu, wasu hudu kuma suka ji rauni sakamakon wasu ‘yan bindiga da suka kai hare-hare daban-daban a kan kananan hukumomin Chikun, Giwa da Kajuru na jihar Kaduna.
Samuel Aruwan, kwamishanan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, ya bayyana abubuwan da suka faru a rahotannin da hukumomin tsaro suka gabatarwa gwamnati.
"A Kan Hawa Zankoro, kusa da Unguwan Yako a karamar hukumar Chikun, wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun harbi wata mota, daga nan kuma sai ta tarwatse, ta kai ga mutuwar mutane shida, sannan wasu hudu suka ji rauni," in ji shi.
Asali: Legit.ng