Gwamnatin Buhari na shirya kashe N396bn kan rigakafin Korona, Ministar Kudi

Gwamnatin Buhari na shirya kashe N396bn kan rigakafin Korona, Ministar Kudi

- Gwamnatin tarayya na shawarin kashe makudan kudade domin sayen allurar rigakafin Korona

- Gwamnatin za ta kashe kudaden da suka haura Naira biliyan 396 a cikin shekarun 2021 da 2022

- Gwamnati ta kuma bayyana cewa, ana iya samun ragakafin sakamakon tallafi da ake samu daga kamfanoni masu zaman kansu

Gwamnatin Tarayya tana tsara kashe Naira biliyan 396 don yin allurar rigakafin Korona a shekarar 2021 da 2022, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ministar Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Laraba bayan taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta Tarayya, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

KU KARANTA: Gobarar kasuwar Katsina: An tara gudunmawar N170m zuwa yanzu, in ji gwamna Masari

Gwamnatin Buhari na shirya kashe N396bn kan rigakafin Korona, Ministar Kudi
Gwamnatin Buhari na shirya kashe N396bn kan rigakafin Korona, Ministar Kudi Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Zainab ta bayyana cewa wannan adadi na iya raguwa matuka kasancewar Gwamnatin Tarayya na karbar karin gudummawar allurar rigakafin daga kamfanoni masu zaman kansu.

Ta kara da cewa Ma’aikatar Lafiya na aiki kan cikakkun bayanai game da gibin da za a bukaci Gwamnatin Tarayya ta cika a aikin yin allurar rigakafin.

Ta kuma bayyana cewa girman kasafin kudin da aka gabatar wanda bangaren zartarwa da bangaren majalisa suka amince dashi har yanzu ba a warware shi ba, saboda Ma'aikatar Tsaro da Lafiya, har yanzu ba ta ba da cikakken bayani game da kayan aikin sojan ba.

KU KARANTA: Lauya ya nemi kotu ta yankewa Zakzaky da matarsa hukunci daidai da laifinsu

A wani labarin, Makonni uku bayan da Najeriya ta fara yi wa ’yan Najeriya allurar rigakafin Korona, a karshe jihar Kogi za ta fara bai wa mazauna yankin damar yin allurar, Vanguard News ta ruwaito.

Saka Haruna, kwamishinan lafiya na jihar, ya ce jihar za ta karbi allurar rigakafin kuma za a fara fitar da ita daga baya. Haruna ya ce jihar ta shirya tsaf don fara aikin rigakafin.

"Mun yi aikin shirye-shirye kuma komai ya kammala da NPHCDA."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.