Babu wanda ya dauki Buhari da muhimmanci, hatta shugabannin hafsun soji, wani sanata
- Wani sanata ya soki yadda shugaba Muhammadu Buhari ke daukar matsalar rashin tsaro
- Ya ce shugaban kawai umarni yake bayarwa a murkushe 'yan ta'adda kuma ba daukar mataki
- Ya kuma zargi shugabannin hafsun sojojin kasar da rashin daukar maganarsa da muhimmanci
Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya soki yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke daukar matsalar rashin tsaro, yana mai cewa babu wanda ya dauki maganar Buhari da muhimmanci hatta shugabannin hafsin soji.
Abaribe ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata hira na shirin gidan talabijin na Channels; Siyasar Yau.
“Me yasa za mu dauke shi (Shugaba Muhammadu Buhari) da muhimmanci? Kwana daya bayan da ya ce ba za mu kara yarda da duk wadannan sace-sacen ba, wannan zai zama na karshe, sun yi satar karshe,” inji shi.
KU KARANTA: Mutum 8 sun mutu, 4 sun ji rauni a harin 'yan bindiga a jihar Kaduna
“Kuma wadancan mutanen suna nan har yanzu; har yanzu ana ci gaba da tsare wadanda ba su ji ba basu gani ba.
"Kullum yana kan yin bayani. Duk lokacin da wadannan abubuwan suka faru, ba abin da ake yi. Don haka a bayyane yake babu wanda ya dauke shi da muhimmanci kan lamarin. Ko shugabannin sojoji, bana tsammanin suna wahalar da kansu.
“Wannan shi ne kusan karo na sama da goma da muke jin Shugaban yana bayar da umarnin murkushewa. Duk tsawon lokacin Buratai a matsayinsa na Shugaban Hafsun Sojoji, koyaushe yana bayar da umarnin murkushewa ne saboda haka yanzu ma ya sake ba da wani."
Najeriya na fama da jerin matsalolin tsaro wadanda suka hada da ta'addanci, 'yan ta'adda, 'yan bindiga, kungiyoyin asiri da sauransu a wasu sassan kasar.
Kasar ta kwashe fiye da shekaru goma tana fama da ta'addanci, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 36,000 tare da raba dubban daruruwa da muhallinsu a arewa maso gabashin kasar.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari na shirya kashe N396bn kan rigakafin Korona, Ministar Kudi
A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta gayyaci mambobin kungiyar likitocin kasa (NARD) zuwa wani ganawa da nufin kaucewa yajin aikin da suka shirya farawa a ranar Alhamis, 1 ga Afrilu, Daily Trust ta ruwaito.
Ministan kwadago da samar da ayyuka, Chris Ngige, wanda ya bayyana hakan ta bakin kakakin ma’aikatar, Charles Akpan, ya ce za a gudanar da zaman ne da karfe 3 na yammacin Laraba, a hedkwatar ma’aikatar dake Abuja.
Yayin da Ngige ne zai jagoranci wakilan gwamnati, mambobin kungiyar ta NARD ana sa ran shugabanta ne, Uyilawa Okhuaihesuyi zai jagorance ta.
Asali: Legit.ng