Bayan tafiyar Buhari Landan duba lafiyarsa, gwamnati za ta zauna da likitoci
- Gwamnatin tarayyata nemi zaman tattaunawa da kungiyar likitoci kan batun yajin aiki
- Kungiyar likitocin ta bayyana shiga yajin aiki a anar Alhamis idan ba a biya bukatunsa ba
- Tafiyar shugaban kasa zuwa Landan ke da wuya aka nemi zaman tattaunawa don jin matsalolinsu
Gwamnatin tarayya ta gayyaci mambobin kungiyar likitocin kasa (NARD) zuwa wani ganawa da nufin kaucewa yajin aikin da suka shirya farawa a ranar Alhamis, 1 ga Afrilu, Daily Trust ta ruwaito.
Ministan kwadago da samar da ayyuka, Chris Ngige, wanda ya bayyana hakan ta bakin kakakin ma’aikatar, Charles Akpan, ya ce za a gudanar da zaman ne da karfe 3 na yammacin Laraba, a hedkwatar ma’aikatar dake Abuja.
Yayin da Ngige ne zai jagoranci wakilan gwamnati, mambobin kungiyar ta NARD ana sa ran shugabanta ne, Uyilawa Okhuaihesuyi zai jagorance ta.
KU KARANTA: Zulum ya yiwa 'yan gudun hijira a Munguno goma na arzika
”Mai girma Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, zai gana da Shugabannin Kungiyar Likitocin Kasa da Wakilan Gwamnatin Tarayya. An shirya ganawar kamar haka: Laraba, 31 ga Maris 2021,” kamar yadda gayyatar ta fada a hukumance.
A ranar Laraba fadar Shugaban kasa ta ce likitocin da suka yi barazanar shiga yajin aikin, gwamnati ta sauraresu kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya fita daga kasar don duba lafiyarsa.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ne ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana a shirin ‘Siyasar Yau na gidan Talabijin din Channels.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin za ta kuma kafa wani katafaren asibiti a Abuja.
Yayin da cutar ta Korona kashi na biyu ta barke, likitocin sun yi barazanar fara yajin aiki na sai Baba ya gani idan gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatunsu.
KU KARANTA: Ku mamaye bakin asibitin da Buhari zai kasance, Sowore ga 'yan Najeriyar Burtaniya
A wani labarin, Makonni uku bayan da Najeriya ta fara yi wa ’yan Najeriya allurar rigakafin Korona, a karshe jihar Kogi za ta fara bai wa mazauna yankin damar yin allurar, Vanguard News ta ruwaito.
Saka Haruna, kwamishinan lafiya na jihar, ya ce jihar za ta karbi allurar rigakafin kuma za a fara fitar da ita daga baya.
Haruna ya ce jihar ta shirya tsaf don fara aikin rigakafin. "Mun yi aikin shirye-shirye kuma komai ya kammala da NPHCDA."
Asali: Legit.ng