Yanzu Yanzu: An damke sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki a kasar Nijar
- An dan samu ci gaba game da zakulo wadanda ke da alhakin yin harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar
- Jami'an tsaro sun damke sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin
- Majiyoyin kasar waje sun yi ikirarin cewa an ji karar harbe-harben a kusa da harabar fadar shugaban kasa a safiyar ranar Laraba, 31 ga watan Maris
Rahotanni sun kawo cewa an damke wasu sojoji a Jamhuriyar Nijar bayan sun yi yunkurin tunkudar da zababbiyar gwamnatin kasar ta hanyar yin juyin mulki.
A safiyar yau Laraba, 31 ga watan Maris ne aka wayi gari da fargabar a kasar inda aka dauki tsawon lokaci ana harbe-harben bindiga a babban birnin Yamai.
Mazauna birnin sun ce, sun kwashe tsawon dare suna jiyo karar harbe-harben bindiga a kusa da fadar shugaban kasar.
KU KARANTA KUMA: Abun farin ciki: Ma’aurata na shirin tarban dansu na fari bayan shekaru 25 da aure
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake saura kwanaki biyu a rantsar da Bazoum Mohamed a matsayin sabon shugaban kasar.
Mazauna birnin sun ce, da misalin karfe uku na dare aka yi ta harbe-harbe da manya da kananan makamai, inda aka dauki tsawon minti 20 ana barin wuta.
Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta ce, tuni aka damke sojojin da ake zargi da kulla-kullan juyin mulkin da bai yi nasara ba, kafar labarai ta RFI ta ruwaito.
Sai dai kuma sashin Hausa na BBC ta ruwaito daga kafofin yaɗa labaran Faransa cewa Sojan da ake zargi da jagorantar juyin mulki a Jamhuriyar Nijar a daren Laraba ya tsere.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Mohamane Ousmane ke ci gaba da ikirarin cewa, shi ya lashe zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka gudanar a ranar 2 ga watan Fabrairu duk da cewa an tabbatar da nasarar Bazoum.
Ousmane ya bukaci magoya bayansa da su gudanar da zanga-zangar lumana a yankunan kasar, amma hukumomin Nijar sun haramta gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati a ranar Laraba.
KU KARANTA KUMA: Kyawawan hotunan ma’auratan da suka raya sunnah watanni 8 bayan haduwarsu a Twitter
A baya mun kawo cewa an yi yunkurin juyin mulki a Jumhuriyar Nijar, sai dai kuma ba a cimma nasarar hakan ba.
Shashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa an jiyo karar harbe-harben bindiga a kusa da fadar Shugaban kasar da ke birnin Yamai.
An kuma tattaro cewa wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje dake birnin na Yamai sun yi kira ga ma'aikatansu da su zauna a gida.
Asali: Legit.ng