Kyawawan hotunan ma’auratan da suka raya sunnah watanni 8 bayan haduwarsu a Twitter

Kyawawan hotunan ma’auratan da suka raya sunnah watanni 8 bayan haduwarsu a Twitter

- Wasu masoya biyu sun ci moriyar kulla zumunci kamar yadda matar ta ce sun raya sunnah ‘yan watanni kadan bayan sun zama abokai a shafin Twitter

- Mutane da dama sun cika da al’ajabi kan yadda alaƙar tasu ta kullu cikin sauri har ta kai ga aure

- Mabiya shafin Twitter sun taya ma’auratan murna, inda suka yi masu fatan samun nasarori a rayuwar aurensu

Wata 'yar Najeriya da ke amfani da shafin Twitter @Raahmatuallah ta yi farin ciki kan manhajar bayan ta yi aure da burin ranta.

A wani wallafa da tayi a ranar Asabar, 27 ga Maris, matar wacce ke cike da farin ciki ta bayyana cewa sun yi aure ne bayan sun hadu da junansu a Twitter na tsawon watanni 8.

KU KARANTA KUMA: 2023: Takarar Tinubu ta samu gagarumin goyon baya daga gwamnonin arewa da masu ruwa da tsaki

Kyawawan hotunan ma’auratan da suka raya sunnah watanni 8 bayan haduwarsu a Twitter
Kyawawan hotunan ma’auratan da suka raya sunnah watanni 8 bayan haduwarsu a Twitter Hoto: @Raahmatuallah
Asali: Twitter

Matashiyar ta wallafa hotunan bikin nasu tare da mijinta a sanye da kayan sojoji. An yi mata kwaliyya sanye da farin kayan amare.

Mata da dama sun shiga ɓangaren sharhinta suna tambayar yaushe mazajensu na Twitter za su gano su kamar yadda ta samo nata.

Kalli wallafar tata a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin sharhin da mabiyanta suka yi a kasa

@hafceeeabbas ta ce:

"@fatee_lawal tabbas muna amfani da Twitter mara kyau. Kalle su masha Allah ..."

@Tawakaalitu tayi tambaya:

"Ina taya ku murna ... mijina na twitter ina kake?"

@ Blen42661309 ta ce:

"Kawai ma shaa Allah. Bai san mutane na iya soyayya a Twitter ba kuma su yi aure. To ina taya ma'aurata murna."

KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun ceto mutum 8 da aka yi garkuwa da su, sun kwato makami a Kaduna

@__Aminasanusi tace:

"Allah ya baku duk wani farin ciki na duniya da na lahira ..HML."

@IsseyTee ya ce:

"Duk da haka, girman kan wasu mutane ba zai taba ba su damar amsa sakonnin DM dinsu ba ..."

@ JoshuaSolomonA1 ya ce:

"Ina taya ku murna, Allah Madaukakin Sarki ya albarkaci sabon gidan ku."

KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun ceto mutum 8 da aka yi garkuwa da su, sun kwato makami a Kaduna

A wani labarin, barayi sun yi wa fitacciyar mawakiya Giselle Knowles-Carter, mai yara uku, satar kayayyaki masu daraja da kudinsu ya kai Dallar Amurka miliyan daya, The Punch ta ruwaito.

A cewar yan sandan, yan fashin sun sace jakunkuna na alfarma, da tufafi masu tsada da kudinsu ya dara dalla miliyan daya daga wurin da Beyonce ke ajiya a Los Angeles.

An kuma kai hari a wurare uku da Beyonce ke ajiya a Los Angeles a lokuta daban-daban cikin wata daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel