'Yan bindiga sun fatattaki 'yan Banga a Adamawa, sun sace wasu manyan mutane biyu

'Yan bindiga sun fatattaki 'yan Banga a Adamawa, sun sace wasu manyan mutane biyu

- Wasu gungunn 'yan bindiga sun kai hari wani yankin jihar Adamawa da safiyar ranar Lahadi

- An ruwato cewa, 'yan bindigan sun sace wasu fitattun mutane biyu a yankin bayan fatattakar 'yan banga

- Tuni aka sanar da hukumar 'yan sanda, inda ta shaida cewa, ta fara bincike kan farywar lamarin

Wasu mahara dauke da bindiga sun kaddamar da wani hari a tsakar dare a garin Kojoli da ke karamar hukumar Jada a jihar Adamawa inda suka yi awon gaba da wasu mazauna garin biyu, jaridar Punch ta ruwaito.

Wani dan asalin garin, Dokta Umar Ardo, ya ce ‘yan bindigan sun isa garin ne da misalin karfe 1 na safiyar Lahadi kuma suka yi awon gaba da wasu fitattun mutane biyu bayan sun fatattaki 'yan banga da ke yankin.

KU KARANTA: Gwamnonin Arewa sun taya Bola Tinubu murnar cika shekara 69

'Yan bindiga sun fatattaki 'yan Banga a Adamawa, sun sace wasu manyan mutane biyu
'Yan bindiga sun fatattaki 'yan Banga a Adamawa, sun sace wasu manyan mutane biyu Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

“A karo na sama da goma, 'yan bindiga a safiyar yau sun mamaye mahaifata, Kojoli. Sun afkawa Banja, wani yankin da galibi fulani suke zaune, cikin adadi mai yawa dauke da manyan bindigogi, cikin sauki suka fi karfin 'yan banga na yankin.

“An ruwaito cewa sun tafi kai tsaye zuwa gidan Alhaji Bajika, Sarki Shanu na Kojoli, kuma suka yi awon gaba dashi.

“Hakazalika, Dr Denis Malum, likitanmu na dabbobi, an sace shi a cikin gidan kiwonsa da ke kusa da garin Nyagang. Don kiyaye bayanai, an sanar da 'yan sanda abubuwan da suka faru kuma sun ce sun fara bincike," in ji Ardo.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar ya ci tura, saboda layin wayarsa ba ya shiga.

KU KARANTA: Jihar Kano ta fi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya, in ji Tinubu

A wani labarin, Yakin da Najeriya ke yi na rashin tsaro zai samu ci gaba nan ba da dadewa ba kasancewar kamfanin mutum-mutumi na farko a Najeriya, Robotic and Intelligence Nigeria (RAIN) ya shirya tsaf don fitar da wata fasahar bin diddigi don yaki da masu satar mutane da 'yan bindiga.

Wanda ya kirkiro kamfanin, Dr. Olusola Ayoola, ne ya bayyana kokarin samar da manhajar a garin Ibadan a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce masanan wadanda ke kan matakin kammalawa za su kara saukaka ayyukan sojojin Najeriya da sauran jami'an tsaro a kokarin da suke yi na kawo karshen satar mutane da hare-haren 'yan bindiga a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel