Bidiyon wani matashi ya shirya tsaf ya sanya suit ya tafi tallan Goro

Bidiyon wani matashi ya shirya tsaf ya sanya suit ya tafi tallan Goro

- A wani bidiyo, matashi ya bayyana yadda sanya sutura suit ke burgeshi har ya fara sakawa

- Matashin mai tallan goro sai da ya shirya tsaf ya sanya suit ya tafi tallan goro a cikin gari

- A cikin bidiyon ya bayyana irin mutanen da ya burge da yin haka, ciki har da Shehu Sani

Wasu mutane na sanya suturar suit lokacin da za su tafi ofis ko wasu lokuta na musamman, kamar biki da sauransu.

Ga wasu mutanen kuwa, - musamman 'yan sanda na sirri da sauran jami'an tsaro - suit da wando kamar inifom ne garesu, donin akan gansu dashi lokuta daban-daban.

KU KARANTA: Bayan tafiyar Buhari Landan duba lafiyarsa, gwamnati za ta zauna da likitoci

Bidiyon wani matashi da sai ya shirya tsaf kamar zai tafi ofis ya dauki tallan goro
Bidiyon wani matashi da sai ya shirya tsaf kamar zai tafi ofis ya dauki tallan goro Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar jami'an tsaro, Zubairu Suleiman mai shekaru 24 ya yi imani da sanya suit, domin kuwa kafin ya fita aiki sai da ya tabbatar da ya shirya tsaf ya sanya kwat, wando har ma da madaurin wuya.

A cikin wannan bidiyon, Sulaiman ya yi bayanin yadda ya fara sanya irin wannan sutura, da kuma dalilin da yasa yake sanyawa.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kogi ta amince da karbar allurar rigakafin Korona

A wani labarin, A shekara 62, yawancin talakawa mantawa suke da batun makaranta gaba daya su dukufa su mai da hankali kan tsufa da more rayuwa tare da jikokinsu.

Ga Maureen Ngoma ta kasar Zambiya kuwa, labarin ya sha ban-ban, domin tsufa ya zama farkon sabon salo a gare ta a fannin ilimi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.