Gwamnatin jihar Kogi ta amince da karbar allurar rigakafin Korona

Gwamnatin jihar Kogi ta amince da karbar allurar rigakafin Korona

- A karshe gwamnatin jihar Kogi ta amince da yiwa 'yan jihar ta allurar rigakafin Korona

- Jihar ta bayyana cewa, ana kokarin samar da allurar domin fara yin ta ga mutanen jihar

- Sai dai, gwamnatin jihar ta ce babu wanda za a tilasta kan dole sai ya karbi allurar ta Korona

Makonni uku bayan da Najeriya ta fara yi wa ’yan Najeriya allurar rigakafin Korona, a karshe jihar Kogi za ta fara bai wa mazauna yankin damar yin allurar, Vanguard News ta ruwaito.

Saka Haruna, kwamishinan lafiya na jihar, ya ce jihar za ta karbi allurar rigakafin kuma za a fara fitar da ita daga baya.

Haruna ya ce jihar ta shirya tsaf don fara aikin rigakafin. "Mun yi aikin shirye-shirye kuma komai ya kammala da NPHCDA."

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamna ya Ganduje ya raka Bola Tinubu zuwa fadar Sarkin Kano

Gwamnatin jihar Kogi ta amince da karbar allurar rigakafin Korona
Gwamnatin jihar Kogi ta amince da karbar allurar rigakafin Korona Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Ya ce duk wanda ke son karbar allurar zai karba kuma ba wanda za a tilasta wa yin rigakafin.

Haruna ya ce za a sanar da wasu shirye-shirye game da batun yin allurar rigakafin lokacin da aka samar da ita.

Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi ya sha musanta wanzuwar Korona a jihar Kogi, yana mai cewa allurar rigakafin ba ita ce babbar damuwar jihar ba.

Bello da Shugaban hukumar NPHCDA, Dokta Faisal Shuaib, sun hadu a ranar Litinin don tattaunawa kan ci gaban da ke kusa da samar da wajen sanyi don adana allurar rigakafin da samar da tsaronta a jihar.

KU KARANTA: Ku mamaye bakin asibitin da Buhari zai kasance, Sowore ga 'yan Najeriyar Burtaniya

A wani labarin daban,Hukumar NCDC ta ruwaito cewa, mutane 48 ne kadai suka kamu da cutar ta Korona daga jihohi 8 a ranar Litinin, wata alama kuma da ke nuna cewa mai yiwuwa kwayar cutar na neman fita daga Nijeriya, PM News ta ruwaito.

Sabanin haka an bada rahoton kamuwar mutane sama da 104 a ranar Lahadi.

Daga cikin sabbin wadanda suka kamu 48, Legas tana da 13 sai kuma Kaduna mai mutum 7. Har ila yau, Nasarawa ta bayar da rahoton kamuwar mutane bakwai, Kano 6, Kwara 5, Ondo 4, Akwa Ibom 3 sai kuma Osun 3.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.