Wata Sabuwa: Yan sanda sun fara bincike kan Musabbabin mutuwar shanu 22 a Ondo

Wata Sabuwa: Yan sanda sun fara bincike kan Musabbabin mutuwar shanu 22 a Ondo

- Rundunar yan sanda reshen jihar Ondo sun sha alwashin binciko musabbabin mutuwar shanu 22 a jihar.

- Ana zargin shanun sun sha guba ne a cikin ruwa, ya yin da ake zargin wasu mutane masu hassada da mai shanun ne suka saka musu gubar

- Sai dai gwamnati tace zatayi duk me yuwu wa wajen tabbatar da cewa mutane ba su ci naman shanun ba

Rundunar 'yan sanda a jihar Ondo ta buɗe sabon babin bincike kan musabbabin mutuwar shanu 22 a Akungba-Akoko karamar hukumar Akoko dake jihar Ondo.

KARANTA ANAN: Ameachi Ya Faɗa Abin Da Yasa Ya Tafi Nijar Ya Roƙa a Bari Nigeria Ta Gina Layin Dogo Zuwa Maraɗi Kyauta

Lamarin mara daɗi na mutuwar shanun ya jefa mutanen yankin cikin ɗari-ɗari, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Shanun da abun ya faru da su mallakin wani mutum ne mai suna Ibrahim Salisu, kuma ana jita-jitar cewa wasu mutane dake hassada da Mr. Salisu ne suka sama shanun guba.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Ondo, DSP Tee-Leo Ikoro, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Channels TV ta wayar salula.

Wata Sabuwa: Yan sanda sun fara bincike kan Musabbabin mutuwar shanu 22 a Ondo
Wata Sabuwa: Yan sanda sun fara bincike kan Musabbabin mutuwar shanu 22 a Ondo Hoto: @channelstv
Source: Twitter

Ya kuma bayyana cewa shanun an basu gubar ne a cikin ruwa, kuma ya tabbatar da cewa zasu tsananta bincike akan lamarin.

KARANTA ANAN: Alkali ya dakatar da NCC, Pantami daga garkame layukan waya saboda rashin NIN

Lokacin da yake martani kan lamarin, mai baiwa gwamnan jihar shawara kan al'amuran tsaro, Jomoh Dojumo, ya ce makiyayan sun yanke shawarar yanka shanun daga lokacin da suka fahinci sun sha guba.

Yace gwamnati ta shirya duk wani abu da yakamata don tabbatar da ba'a siyar da naman shanun ga mutanen jihar ba.

A cewar sa idan tabbas shanun sun sha guba a ruwa kamar yadda ake jita-jita to namansu zai yi illa ga lafiyar mutane.

A wani labarin kuma Rundunar Yan sanda ta kama mutum 14 da zargin aikata manya-manyan Laifuka a jihar Ondo

Rundunar yan Sandan ƙasar nan reshen jihar Ondo ta bayyana cafke mutane 14 da zargin aikata manyan laifuka a jihar.

Yan sandan sun ce mutanen da aka kama ana zargin su da aikata laifukan da suka haɗa da, satar mutane, fashi da makami da kuma sauran ayyukan ta'addanci.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel