Rundunar Yan sanda ta kama mutum 14 da zargin aikata manya-manyan Laifuka a jihar Ondo

Rundunar Yan sanda ta kama mutum 14 da zargin aikata manya-manyan Laifuka a jihar Ondo

- Rundunar yan Sandan ƙasar nan reshen jihar Ondo ta bayyana cafke mutane 14 da zargin aikata manyan laifuka a jihar

- Yan sandan sun ce mutanen da aka kama ana zargin su da aikata laifukan da suka haɗa da, satar mutane, fashi da makami da kuma sauran ayyukan ta'addanci

- Kwamishinan rundunar jihar ya ce jami'ansa sun yi matuƙar ƙoƙari idan ka haɗa da ayyukan takwarorinsu dake wasu jihohin ƙasar nan

Rundunar yan sanda a jihar Ondo ta kama mutane 14 da zargin aikata manya-manyan laifuka a jihar.

An zargin mutanen da aka kama da aikata laifuka da suka haɗa da: fashi da makami, satar mutane domin neman kuɗin fansa, sace-sace da dai sauransu.

KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tashi, ya tafi kasar Ingila

Hukumar ta yan sanda na tsare da mutanen ne a babban ofishin ta dake Akure, babban birnin jihar Ondo, jaridar Punch ta ruwaito.

Kwamishinan yan sandan jihar, Mr. Bolaji Salami, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a tsakanin watan Fabrairu zuwa watan Maris da muke ciki.

A rahoton jaridar Punch, kwamishinan yan sandan jihar ya bayyana waɗanda aka kama da suka haɗa da:

Isaac Monday, Ajilogba Wande, Omisakin Samson, Abiodun Osuntimehin, Rasheed Oke, Abiwo Gbemiteke da kuma Martins Aliu.

Rundunar Yan sanda Sun kama mutum 14 da zargin aikata manya-manyan Laifuka a jihar Ondo
Rundunar Yan sanda Sun kama mutum 14 da zargin aikata manya-manyan Laifuka a jihar Ondo Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Sauran sune: Oluremi Olubunmi, Nathaniel Henejer, Abiwo Gbemiteke, Gbenro Adetuyi, Jimoh Blessing, Dennis Okoh da kuma Sunday Asaba.

KARANTA ANAN: Bayan rikicin Hausawa da Yarabawa zaman lafiya ya dawo a jihar Oyo - Yan sanda

Salami yace: "Idan kaduba ayyukan da muka yi cikin ƙanƙanin lokaci, Rundunar mu ta jihar Ondo ta yi matuƙar ƙoƙari idan aka haɗa da ayyukan wasu jihohin a ƙasar nan."

"Haka zalika zan iya cewa a wannan ƙanƙanin lokacin, Jami'an sun fara shawo kan lamarin satar mutane,da kuma fashi da makami waɗanda suka addabi wannan jihar tamu."

Kwamishinan ya ƙara da cewa, duk wani ɗan fashi ko mai satar mutane da ya taso daga wata jiha ya dawo nan jihar dan yin aikinsa to ina tabbatar da cewa yanzin ya fara dana sanin zuwansa.

A cewarsa: "Jami'an mu tare da haɗin guiwar wasu hukumomin tsaro sun fara kawar da irin waɗannan mutanen da kuma ta'addancin su."

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta bada hutu ranar Juma'a da Litinin don murnar Easter

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Juma'a, 2 ga Afrilu da Litnin 5 ga Afrilu 2021, matsayin ranar hutu don murnar bikin Ista na bana.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ke da hakkin sanar da ranakun hutu a Najeriya.

Source: Legit.ng

Online view pixel