Ameachi Ya Faɗa Abin Da Yasa Ya Tafi Nijar Ya Roƙa a Bari Nigeria Ta Gina Layin Dogo Zuwa Maraɗi Kyauta

Ameachi Ya Faɗa Abin Da Yasa Ya Tafi Nijar Ya Roƙa a Bari Nigeria Ta Gina Layin Dogo Zuwa Maraɗi Kyauta

- Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri na Nigeria ya ce sai da ya tafi Nijar da kansa ya roke su su amince Nigeria ta gina layin dogo zuwa Maradi

- Ministan ya ce ya zama dole ya yi hakan ne domin yin layin dogon zai amfani Nigeria sosai wurin kasuwanci da inganta tattalin arziki

- Ya ce yan kasuwan Nijar su kan zagaye Nigeria su shigo da kayansu ta wasu kasashe saboda batun rashin kyawun titi, tsaro da wasu abubuwam amma layin dogon zai magance hakan

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya ce sai da ya tafi Jamhuriyar Nijar da kansa ya roki kasar ta bari Nigeria ta gina layin dogo daga jihar Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Amaechi ya yi wannan furucin ne a hirar da aka yi da shi a shirin 'News Night' a gidan talabijin na Channels Television a ranar Litinin.

Ameachi Ya Faɗa Abin Da Yasa Ya Tafi Nijar Ya Roƙa a Bari Nigeria Ta Gina Layin Dogo Zuwa Maraɗi Kyauta
Ameachi Ya Faɗa Abin Da Yasa Ya Tafi Nijar Ya Roƙa a Bari Nigeria Ta Gina Layin Dogo Zuwa Maraɗi Kyauta. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji

Ana sa ran layin dogon zai bi ta Kano zuwa Dutse ya shiga Katsina ta garin Jibia sannan ya tsaya a Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Da aka masa tambaya kan muhimmancin aikin da ya sa har ya tafi Maradi da kansa ya roki gwamnatin Nijar, Amaechi ya yi bayanin cewa Nijar zagaye ta ke da kasa don haka ta dogara da tashoshin kan tudu ne domin kasuwanci hakan tana bukatar bi ta wasu kasashen domin saye da sayarwa.

Ministan ya ce rashin kyawun tituna, yan fashi da jami'an tsaro masu karbar cin hanci, Nijar da Chadi sun koma shigo da kayayyaki ta kasashen Jamhuriyar Benin, Ivory Coast, Ghana da Togo.

Ya ce sabon layin Dogon zai taimakawa Nigeria yin gasa a wannan bangaren da habbaka tattalin arzikinta.

KU KARANTA: Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Lakaɗawa Duka Har Suka Zubarwa Wani Haƙoransa

Ameachi ya kara da cewa, "Me yasa ba ku shigo da kaya ta Nigeria? Sun ce titunan ku ba su da kyau. Layin dogon zai magance hakan. Sun ce Kwastam na wahalar da su, suna karbar kudaden da ba a karba a Jamhuriyar Benin.

"Sun ce idan kuma sun wuce Kwastam, akwai yan sanda a tituna, da Immigration da yan fashi sannan garuruwa sukan karbi nasu kudin. Don haka sun gwammace su tafi kasashen da akwai tsaro kuma ga arahar yin kasuwanci.

"Abinda muke cewa shine zamu tafi Maradi mu gina ofisoshi da dakunan ajiye kaya, za ku ajiye kayanku a can, ku yi harkokinku da kwastam, Immigration da yan sanda a Maradi. Da kun saka kayanku zai tafi Legas nan take kuma baku bukatar harka da jami'an Nigeria don kunyi abinda ya dace da jami'an tsaron Maradi."

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel