Alkali ya dakatar da NCC, Pantami daga garkame layukan waya saboda rashin NIN

Alkali ya dakatar da NCC, Pantami daga garkame layukan waya saboda rashin NIN

- Kotu ta hana a toshe layin wayar da ba ayi wa rajistar lambar NIN ba

- Alkali ya bada umarni a tsawaita wa’adin yin rajistar sai watan Mayu

- An zartar da wannan hukunci ne bayan wani Lauya ya shigar da kara

Jaridar Punch ta ce babban kotun tarayya da ke Legas ya hana gwamnatin tarayya toshe layukan wayoyi watau SIM da ba ayi masu rajistar lambar NIN ba.

Ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani ta bada umarni ta hannun hukumar NCC, ta bukaci kamfanoni su rufe duk wani layin wayar da bai da lambar NIN.

Wannan mataki da NCC ta dauka ya sa tsohon mataimakin shugaban kungiyar NBA na kasa, Monday Ubani, ya kai kara kotu, ya na kalubalantar gwamnati.

KU KARANTA: Dole a hada kowane layi da lambar NIN din mai salula - Gwamnati

Babban lauya Monday Ubani ya nemi a hana NCC toshe layukan da ba a hada su da lambar ta NIN ba.

Ubani ya hada gwamnatin tarayya, Ministan shari’a, hukumar NCC, da kuma Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami, a karar da ya shigar.

Lauyan ya fada wa kotu cewa wa’adin makonni biyun da aka bada ya yi kadan, wanda hakan zai matsa wa al’umma, tare da shiga hakkinsu na zama ‘yan kasa.

Har ila yau, Monday Ubani, ya kuma bukaci kotu ta bada umarni a tsawaita wa’adin da aka bada.

KU KARANTA: Ana kokarin maye gurbin lambar BVN da NIN a Najeriya

Alkali ya dakatar da NCC, Pantami daga garkame layukan waya saboda rashin NIN
Shugabannin NCC a taro
Asali: Facebook

A karshe Alkali M.A Onyetenu ya yanke hukunci cewa a tsawaita wa’adin da watanni biyu daga ranar da aka zartar da hukunci, ya ce wa’adin da aka sa ya kure.

Mai shari’a Onyetenu ya karbi kukan lauyan, ya ce kokarin yin rajistar NIN cikin wahala, zai ci karo da sashe na 39 da 41 na tsarin mulki a kan damar ‘yan kasa.

Alkalin ya kuma ce tursasa wa mutane har miliyan 200 yin rajistar lambar NIN ta ‘yan kasa a lokacin da ake fama da annobar COVID-19, zai jefa jama’a cikin hadari.

Kwanaki kun ji yadda Hukumar sadarwan Najeriya, watau NCC ta umurci dukkannin kamfanonin sadarwa su dakatar da rijistar sababbin layukan waya.

NCC ta bada wannan umurnin ne saboda manufar gwamnatin tarayya na duba rumbun wadanda su kayi rajista da kuma tabbatar da cewa kamfanonin na bin dokoki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel