Tafiyar ganin Likita: Buhari ba ya bukatar mika mulki ga Osinbajo - Fadar shugaban kasa

Tafiyar ganin Likita: Buhari ba ya bukatar mika mulki ga Osinbajo - Fadar shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa ta ce ba dole bane sai Shugaban kasa Buhari ya mika mulki ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ba

- Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan yayinda yake amsa tambaya kan ko Buhari ya mika mulki ga Osinbajo

- Ya ce ko kadan shugaban kasar bai sabawa dokokin kasar ba ta hanyar kin mika ragamar mulki ga mataimakinsa

Bai zama dole ba ga Shugaba Muhammadu Buhari ya mika mulki ga Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, in ji Fadar Shugaban Kasa.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya bayyana a matsayin bako a shirin Politics Today na gidan talbijin din Channels.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya sun yi martani yayin da shekarun Tinubu ya sauka daga 79 zuwa 69 a shafin Wikipedia

Tafiyar ganin Likita: Buhari ba ya bukatar mika mulki ga Osinbajo - Fadar shugaban kasa
Tafiyar ganin Likita: Buhari ba ya bukatar mika mulki ga Osinbajo - Fadar shugaban kasa Hoto: Channels TV
Source: UGC

Ya yi bayanin cewa Shugaba Buhari bai sabawa dokokin kasar ba ta hanyar kin mika ragamar mulki ga Farfesa Osinbajo yayin da ya bar kasar na wasu kwanaki.

"Shi (Buhari) zai ci gaba daga duk inda yake," in ji Shehu lokacin da aka tambaye shi ko Shugaban kasar ya mika ragamar ayyuka ga mataimakin shugaban.

Ya kara da cewa, “Abin da doka ta tanada shi ne cewa Shugaban kasar zai kasance ba ya cikin kasar har na tsawon kwanaki 21 da fiye da haka, to a kan hakan ne ake da garantin mika mulki. A wannan yanayin na musamman, ba bu bukatar haka.”

Yan sa’o’i kafin tattaunawar, Shugaba Buhari ya tashi daga Fadar Shugaban Kasa zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 2:30 na rana inda daga nan ya wuce zuwa Landan don duba lafiyarsa.

KU KARANTA KUMA: Ba zan taba goyon bayan tsawaita mulki ga Shugaba Buhari ba - Lawan

A wani labarin, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya fara zuwa duba lafiyarsa Landan tun kafin ya zama shugaban kasan Najeriya a 2015.

Shehu ya bayyana hakan ranar Talata yayinda yake hira da manema labarai lokacin da jirgin Buhari ya tashi daga tashar jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja.

Yace, "Shugaban kasa yana kokarin amfani da hutun bikin Easter ne. Lokacin da kowa ke hutu ne... Saboda haka zai yi amfani da lokacin wajen duba lafiyarsa."

Source: Legit.ng

Online view pixel