Tun kafin Buhari ya zama shugaban kasa yake zuwa Landan duba lafiyarsa, Garba Shehu

Tun kafin Buhari ya zama shugaban kasa yake zuwa Landan duba lafiyarsa, Garba Shehu

- Malam Garba Shehu ya bayyana dalilin da ya sa Buhari ke zuwa Landan

- Tun da Buhari ya hau mulki, kowace shekara ya kan je Landan duba lafiyarsa

- Wasu yan Najeriya sun bukaci Buhari ya mika mulki ga mataimakinsa

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya fara zuwa duba lafiyarsa Landan tun kafin ya zama shugaban kasan Najeriya a 2015.

Shehu ya bayyana hakan ranar Talata yayinda yake hira da manema labarai lokacin da jirgin Buhari ya tashi daga tashar jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja.

Yace, "Shugaban kasa yana kokarin amfani da hutun bikin Easter ne. Lokacin da kowa ke hutu ne... Saboda haka zai yi amfani da lokacin wajen duba lafiyarsa."

"Wannan abu ne wanda ya dade yana yi shekara da shekaru tun kafin ya hau mulki. Duk shekara yana ganawa da Likitocinsa."

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bada hutu ranar Juma'a da Litinin don murnar Easter

Tun kafin Buhari ya zama shugaban kasa yake zuwa Landan duba lafiyarsa, Garba Shehu
Tun kafin Buhari ya zama shugaban kasa yake zuwa Landan duba lafiyarsa, Garba Shehu Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bada hutu ranar Juma'a da Litinin don murnar Easter

Mun kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga tashar jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja domin zuwa kasar Birtaniya.

Hadimin Buhari kan gidajen talabijin da rediyo, Buhari Sallau, ya bayyana hakan da misalin karfe 3 na rana.

Shahrarren dan fafutuka, Omoyele Sowore, ya shawarci ‘yan Nijeriya da ke Ingila su mamaye asibitin Landan inda Shugaban kasa ke shirin zuwa don duba lafiyarsa.

Sowore ya bayyana tafiyar shugaban zuwa Landan a matsayin barnatar da dukiya, yana mai cewa ya kamata Shugaban kasa ya duba lafiyarsa a asibitin "mai daraja ta duniya" da ya gina tun hawan sa mulki.

Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya mazauna Burtaniya da su mamaye Abuja House da ke Landan inda shugaban zai zauna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng