Ba zan taba goyon bayan tsawaita mulki ga Shugaba Buhari ba - Lawan

Ba zan taba goyon bayan tsawaita mulki ga Shugaba Buhari ba - Lawan

- Sanata Ahmad Lawan ya nesanta kansa daga wani rubutu da aka alakanta da shi

- Shugaban majalisar dattawan ya ce sam bai taba cewa yana goyon bayan tsawaita mulkin Shugaba Muhammadu Buhari har bayan 2023 ba

- Lawan ya ce yana tare da tsarin mulki da ya kayyade wa’adi biyu ga Shugaban kasa kuma ba zai taba yarda ayi masa kwaskwarima ba

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya yi watsi da wani rahoto wanda ya ambato shi yana cewa ba zai damu da yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima ba don ba wa Shugaba Muhammadu Buhari damar ci gaba da mulki bayan 2023.

Lawan, a wata sanarwa daga mai taimaka masa a kafofin yada labarai, Ola Awoniyi, ya ce bai taba yin irin wannan magana ba kafin ko bayan 2019, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban Majalisar Dattawan ya ce yana tare da tsarin mulki da ya kayyade wa’adi biyu ga Shugaban kasa kuma ba zai taba yarda da duk wani yunkuri na gyara shi ba.

Ba zan taba goyon bayan tsawaita mulki ga Shugaba Buhari ba - Lawan
Ba zan taba goyon bayan tsawaita mulki ga Shugaba Buhari ba - Lawan Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Buhari ya ba da umarnin murkushe 'yan fashi, masu satar mutane

Sanarwar ta ce: “Kundin Tsarin Mulki na 1999 yana da matsaya mai karfi kan wa’adin mulkin Shugaban kasa wanda shine muradin mafi yawan yan Najeriya .

““Sashe ne 137(1)b ya tanadi cewa: Mutun na iya cancantar a zabe shi ya zama Shugaban Kasa (b) a zabe shi sau biyu a ofishin.

“Shugaban Majalisar Dattawa bai taba samun wani abu ba daidai ba a cikin wannan tanadi na Kundin Tsarin Mulki kuma a koyaushe yana tsaye kyam a kai.

“Ya kamata a tuna cewa Lawan dan Majalisar Tarayya ne a 2006 lokacin da ta yi fatali da yunkurin tsawaita wa’adin mulkin Shugaban Kasa.

“Abin da Majalisar ta yi a wancan lokaci shi ne daidai da ra’ayin ’yan Najeriya.

“Saboda haka yaudara ce kawai ayi tunanin cewa Lawan zai iya kasancewa cikin masu goyon bayan irin wannan rashin tunanin wanda ba zai taba cimma nasara ba.

“Saboda haka ba yadda za a yi yanzu Shugaban majalisar dattijan ya koma goyon bayan irin wancan yunkuri.

"Don haka, muna umartar jama'a da su yi watsi da tsohuwar sanarwar da aka kirkira wacce ake danganta ta ga Shugaban Majalisar Dattawa kuma yanzu masu yin barna ke yada shi."

KU KARANTA KUMA: Bayan rikicin Hausawa da Yarabawa zaman lafiya ya dawo a jihar Oyo - Yan sanda

A gefe guda, tsohon Sanata, Dino Melaye ya roki Shugaba Muhammadu Buhari ya mika mulki ga Mataimakinsa, Yemi Osinbajo yayin da yake shrin tafiya zuwa Landan don duba lafiyarsa, PM News ta ruwaito.

Fadar Shugaban kasa ta sanar a ranar Litinin cewa Buhari zai yi tafiya zuwa Landan ta kasar Ingila don duba lafiyarsa kuma zai dawo nan da makonni biyu.

Don haka Dino Melaye, a cikin wani sakon Twitter ya ce ya kamata Buhari ya mika mulki ga Mataimakin Shugaban kasa ta hanyar rubuta wasika zuwa ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng