Bayan rikicin Hausawa da Yarabawa zaman lafiya ya dawo a jihar Oyo - Yan sanda

Bayan rikicin Hausawa da Yarabawa zaman lafiya ya dawo a jihar Oyo - Yan sanda

- Hukumar yan sandan jihar Oyo ta yi nasarar kwantar da tarzomar da ta tashi a yankin Apata da ke Ibadan, babbar birnin jihar Oyo

- Kakakin yan sanda a jihar, Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da hakan inda yace ba a jikkata kowa ba

- Mazauna yankin sun ce sunji karar harbe-harbe yayin da bangarorin biyu ke kai wa juna hari

Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta dawo da zaman lafiya a yankin Apata da ke garin Ibadan bayan rikici da aka samu tsakanin Hausawa da Yarabawa.

Kakakin yan sanda a jihar, Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace kawai dan sabani ne aka samu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Buhari ya ba da umarnin murkushe 'yan fashi, masu satar mutane

Bayan rikicin Hausawa da Yarabawa zaman lafiya ya dawo a jihar Oyo - Yan sanda
Bayan rikicin Hausawa da Yarabawa zaman lafiya ya dawo a jihar Oyo - Yan sanda Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Har ila yau ya bayyana cewa babu wanda ya jikkata a rikicin kuma cewa sun yi nasarar shawo kan al’amarin.

Sai dai kuma a wata hira da shashin BBC, mazauna yankin sun bayyana cewa sun ji karar harbe-harbe yayin da bangarorin biyu ke kai wa juna hari.

Wani mazaunin unguwar Sabo ya ce: "Ina kwance kawai na ji mutane sun rugo a guje, da har zan gudu sai na ga daji ne a gabana. Daga baya aka ce Hausawa da Yarabawa ne ke faɗa.

"Na ji harbin bindiga amma dai ban ga wanda aka harba ba da idona."

KU KARANTA KUMA: Shugaban Majalisa ya roki Shugaba Buhari ya jarraba shawarwarin da Tinubu ya bada

A wani labarin, mun ji cewa hankulan mutane sun tashi a garin Ikot Afunga a karamar hukumar Essien Udim a jihar Akwa Ibom a jiya Litinin a yayin da yan daba suka sake cinnawa wani dan sanda mai mukamin sufeta wuta a gidansa.

An gano cewa yan daban sun afka gidan dan sandan mai suna Aniekan misalin karfe 2.30 na dare suka zagaye gidan suka cinna wuta a lokacin yana barci, Vanguard ta ruwaito.

Wannan shine karo na uku da yan daba ke kai wa yan sanda hari a gida da caji ofis a karamar hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel