Ta ya zai yiwu: Shenu Sani ya caccaki batun Tinubu na daukar sojoji miliyan 50

Ta ya zai yiwu: Shenu Sani ya caccaki batun Tinubu na daukar sojoji miliyan 50

- Tsohon sanata Shehu Sani ya caccaki maganar Bola Tinubu na daukar miliyoyin sojoji

- Sanatan ya nuna jin mamaki matuka da irin wannan magana ta fito daga bakin Tinubu

- Ya ce, yana mamakin yadda za a iya daukar nauyin sojojin sa suka kai har miliyan 50

Tsohon sanata Shehu Sani ya mai da martani kimanin awanni ashirin da hudu bayan shugaban jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dauki sojoji miliyan 50 don magance matsalar rashin tsaro a kasar.

Legit.ng ta rahoto cewa Shehu Sani, wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a lokacin majalisar kasa ta takwas, ya yi mamakin dalilin da yasa Tinubu zai yi kira da a dauki sojoji miliyan 50 alhali gwamnatin tarayya na kokawa kan biyan albashin sojoji kasa da dubu 150.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun fatattaki 'yan Banga a Adamawa, sun sace wasu manyan mutane biyu

Shenu Sani ya caccaki batun Tinubu na daukar sojoji miliyan 50 aiki
Shenu Sani ya caccaki batun Tinubu na daukar sojoji miliyan 50 aiki Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 30 ga watan Maris, Sanatan ya yi tambayar cewa:

"Idan har ba mu iya daukar nauyin yadda za mu kula da sojojinmu 150k, ta yaya za mu iya rikewa da kuma daukar nauyin sojoji miliyan 50 dauke da makamai a kan tsarin biyan albashinmu?"

Asiwaju Bola Tinubu ya yi kiran a dauki sojojin miliyan 50 jiya a jihar Kano a wani taron tunawa da ranar haihuwarsa da gudana a jihar.

KU KARANTA: Malaye: Ya kamata Buhari ya mika mulki dungurugum ga Osinbajo kan tafiya Landan

A wani labarin, Shugaban jam'iyyar Bola Tinubu, ya yaba da jihar Kano cewa ita ce jihar da tafi kowacce jiha zaman lafiya a Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ya fadi haka ne a taron bikin maulidinsa na karo na 12 da aka gudanar a jihar Kano don tunawa da ranar haihuwarsa da cikarsa shekaru 69 a duniya.

Tsohon Gwamnan na Jihar Legas ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje game da nasarorin da ya samu musamman a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel