Jihar Kano ta fi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya, in ji Tinubu

Jihar Kano ta fi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya, in ji Tinubu

- Shugaban jam'iyyar APC Tinubu ya yabawa jihar Kano duba da zaman lafiya dake cikinta

- Shugaban na APC ya kuma yabawa gwamna Ganduje kan ayyuka na more rayuwa da yayi

- Ya kuma bayyana rashin jin dadinsa ga shawarar wasu kasashe na hana 'yan kasarsu zuwa Kano

Shugaban jam'iyyar Bola Tinubu, ya yaba da jihar Kano cewa ita ce jihar da tafi kowacce jiha zaman lafiya a Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ya fadi haka ne a taron bikin maulidinsa na karo na 12 da aka gudanar a jihar Kano don tunawa da ranar haihuwarsa da cikarsa shekaru 69 a duniya.

KU KARANTA: Marwa da wasu jami'an NDLEA sunyi gwajin ba-zata na shan miyagun kwayoyi

Jihar Kano ta fi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya, in ji Tinubu
Jihar Kano ta fi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya, in ji Tinubu Hoto: thestreetjournal.org
Asali: UGC

Tsohon Gwamnan na Jihar Legas ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje game da nasarorin da ya samu musamman a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa.

Ya ce, “Jihar da ta fi zaman lafiya ita ce Kano. Da zarar kun samar da zaman lafiya, sada zumunci da kuma damar saka jari zai zo.”

Sai dai, Amurka da sauran kasashen yamma, sun shawarci 'yan kasarsu da su guji zuwa Kano da wasu jihohi 13 saboda matsalar rashin tsaro.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje: Wajibi ne 'yan Najeriya su koma ga Allah

A wani labarin daban, Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya shawarci masu kira ga raba Najeriya da su sake tunani, ya kara da cewa idan Najeriya ta wargaje, dole su bukaci katin biza domin tafiya sassan arewa kamar Kano.

Osinbajo ya fadi haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron tattaunawa na 12 na bikin cika shekaru 69 na Bola Tinubu da aka gudanar a jihar Kano, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.