APC ta yi ikirarin cewa ba ta taba sanin matakin da cin hanci da rashawa ya kai ba a Najeriya

APC ta yi ikirarin cewa ba ta taba sanin matakin da cin hanci da rashawa ya kai ba a Najeriya

- Jam’iyyar APC mai mulki ta hannun Farooq Aliyu ta yi ikirarin cewa ba ta da masaniya game da lalacewar kasar lokacin da ta karbi mulki

- A cewarsa, matakin da cin hanci da rashawa ya kai abin tsoro ne, har ma ta kai abun na yakar gwamnati

- A halin da ake ciki, Aliyu ya ce APC na iya bakin kokarinta don sake daidaita kasar nan

Farooq Aliyu, jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon shugaban marasa rinjaye, a majalisar wakilai ya bayyana cewa jam'iyyar ba ta san matakin da rashawa ya kai ba a Najeriya kafin su hau mulki.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a matsayin bako a gidan Talabijin na Channels. A cewar Aliyu, jam'iyyar ba ta san cewa akwai gagarumin lalacewa a tsarin Najeriya ba.

KU KARANTA KUMA: NBS ta fitar da jerin basusukan da ake bin kowace jihar Najeriya yayin da ya kai N4.2tn

APC ta yi ikirarin cewa ba ta taba sanin matakin da cin hanci da rashawa ya kai ba a Najeriya
APC ta yi ikirarin cewa ba ta taba sanin matakin da cin hanci da rashawa ya kai ba a Najeriya
Asali: Twitter

Jigon na APC ya yi ikirarin cewa matakin tabarbarewar kasar ta kai intaha ta yadda a duk lokacin da gwamnati ta yi kokarin kawo sauye-sauye, rashawa za ta samu hanyar yaki da ita.

Musamman, Aliyu ya caccaki tsohon mataimakin shugaban Najeriya. Ya ce lokacin da Atiku Abubakar ke kan mulki, an karkatar da wasu kudade.

A wani labarin, babban jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bada shawarar yadda za ayi maganin fatara, a farfado da tattalin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya na cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta saki kudi da nufin yakar talauci da rashin aikin yi.

Bola Tinubu ya ce akwai bukatar shugabanni masu rike da madafan iko da ‘yan majalisa su hada-kai, a samu a ga yadda za a kawar da talaucin da ake fama da shi.

Duk a jawabin na sa, Asiwajun na Legas kuma Jagaban na kasar Borgu ya ba gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari shawarar yadda za a magance matsalar tsaro.

Bola Ahmed Tinubu ya roƙi gwamnatin tarayya da ta ɗauki matasa masu jini a jika 50 miliyan cikin aikin soja domin a kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel