Rashin Tsaro: Ku ɗauki Matasa Masu Ɗanyen jini 50 Miliyan aikin Soja, Tinubu ga Gwamnatin Tarayya

Rashin Tsaro: Ku ɗauki Matasa Masu Ɗanyen jini 50 Miliyan aikin Soja, Tinubu ga Gwamnatin Tarayya

- Jagoran Jam'iyya mai mulkin ƙasar nan kuma tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Tinubu, ya kirayi gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa 50 miliyan aikin soja

- Bola Tinubu ya yi wannan kiran ne a taron murnar cikarsa shekaru 69 a duniya wanda ya gudana a jihar Kano

- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya halarci taron ta hanyar amfani da fasahar zamani wato (Virtually) kuma shine ya shugabanci taron.

Jagoran jam'iyya mai mulkin ƙasar nan, Bola Tinubu,ya kirayi gwamnatin tarayya da ta ɗau matasa 50 miliyan aikin soja don magance matsalar tsaro data addabi ƙasar.

KARANTA ANAN: Gwamna Ganduje: Wajibi ne 'yan Najeriya su koma ga Allah

A jawabin da ya yi a wajen taron bikin murnar cikarsa shekaru 69 a duniya, Tinubu yace ɗaukar wannan matakin zai kara taimakawa wajen yaƙi da ta'addanci.

A jawabin da jigon ya yi a wajen taron yace:

"Muna ƙarkashin yan sanda kuma muna fama da matsalar yan fashi da makami, da yan bindiga. A ɗauki matasa masu ɗanyen jiki aikin soja kamar mutum 50 miliyan, abubuwan da zasu ci kamar rogo, ko masara duk zasu samu anan."

"Ku daina cewa jahilci ke damun su, duk mutumin da zai iya riƙe bindiga, zai iya sarrafa ta, kuma zai iya shiryawa ya yi harbi da ita to wannan zai iya gyara babbar mota a gareji."

Rashin Tsaro: Ku ɗauki Matasa Masu Ɗanyen jini 50 Miliyan aikin Soja, Tinubu ga Gwamnatin Tarayya
Rashin Tsaro: Ku ɗauki Matasa Masu Ɗanyen jini 50 Miliyan aikin Soja, Tinubu ga Gwamnatin Tarayya Hoto: @AsiwajuTinubu
Source: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Lagos ɗin ya jinjjina ma matasa musamman waɗanda suke nuna a shirye suke wajen taimakawa a dawo da zaman lafiya a ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Mutum 50 Sun Mutu Bayan Hallartar Casu da 'Yahoo Boy' Ya Haɗa a Legas

Taron wanda ya gudana a jihar Kano anyi masa take da: “Hadin kan mu, arzikin mu: Wajibi ne ga hadin kan kasa don girma da ci gaba”

Taron ya samu halartar shugaban ƙasa Mejo Janar Muhammadu Buhari, wanda shine ya jagoranci taron ta hanyar amfani da fasahar zamani ta (Virtually).

Shugaba Buhari ya jaddada muhimmancin haɗin kai da samar da ƙasa ɗaya, Najeriya, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

Taron ya samu halartar manyan jagororin ƙasar nan ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually), waɗanda suka haɗa da;

Mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osibanjo, shugaban majalisar Dattijai, Ahmed Lawan, Kakakin majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran su.

A wani labarin kuma 'Yan sanda Sun yi ram da wani mutumi da ake zargi da hannu wajen sace Basarake a Jihar Rivers

Rundunar yan sanda a jihar Rivers ta kama wani mutumi mai suna Wariboko Basoene, wanda ake zargin yana da hannu a sace wani Basarake.

An dai sace Sarkin Ikuru dake karamar hukumar Andoni, jihar Rivers, Aaron Miller ne a ranar 21 ga watan Fabrairu a cikin garinsa na Ikuru.

Source: Legit

Online view pixel