Tinubu ya fadawa Buhari: Ka fito da kudi, ka daina matse aljihu yayin da Matasa su ke cikin fatara

Tinubu ya fadawa Buhari: Ka fito da kudi, ka daina matse aljihu yayin da Matasa su ke cikin fatara

- Bola Tinubu ya ba gwamnatin tarayya shawarar yadda za a inganta tattali

- Tsohon Gwamna ya bukaci gwamnatin Muhammadu Buhari ta fito da kudi

- Tinubu ya ce yanzu ba lokaci ba ne da gwamnati za ta tsuke bakin aljihunta

Babban jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bada shawarar yadda za ayi maganin fatara, a farfado da tattalin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya na cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta saki kudi da nufin yakar talauci da rashin aikin yi.

Bola Tinubu ya ce akwai bukatar shugabanni masu rike da madafan iko da ‘yan majalisa su hada-kai, a samu a ga yadda za a kawar da talaucin da ake fama da shi.

KU KARANTA: Tinubu ya yabi Ganduje, ya ce Kano ta fi kowace jiha zaman lafiya

Gawurtaccen ‘dan siyasar ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da majalisar tarayya su dakatar da matakan da su ka kawo na tsuke bakin aljihu.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bada shawarar a dumbuzo kudi saboda a zaburar da tattalin arziki.

Tinubu ya yi wannan bayani ne a garin Kano a lokacin da yake jawabi wajen bikin taya shi murnar cika shekara 69 da aka shirya a ranar 29 ga watan Maris, 2021.

A cewar ‘dan siyasar, ya kamata shugabannin Najeriya su tsara manufofinsu ta yadda za su amfani talaka, ya ce bai dace a bar mutane su yi ta azumi ba.

KU KARANTA: Tsohon Sanatan Kaduna ya taya Tinubu murnar cika shekara 69

Tinubu ya fadawa Buhari: Ka fito da kudi, ka daina matse aljihu yayin da Matasa su ke cikin fatara
Bola Tinubu da Shugaba Buhari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Lokaci ne da za a saki kudi, babu lokacin da za a rika matse bakin aljihu. Babu lokacin da za a rika tsuke tattalin arziki, lokaci ne da za a samar da damammaki.”

“33% na mutane ba su da aikin yi, ka na cewa a cigaba da azumi. Domin lada ake azumi. Mun yi shekaru mu na azumi.” Tinubu ya bukaci ayi koyi da Amurka.

Duk a jawabin na sa, Asiwajun na Legas kuma Jagaban na kasar Borgu ya ba gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari shawarar yadda za a magance matsalar tsaro.

Bola Ahmed Tinubu ya roƙi gwamnatin tarayya da ta ɗauki matasa masu jini a jika 50 miliyan cikin aikin soja domin a kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng