'Yan Najeriya sun kirkiri fasahar bin diddigin 'yan bindiga a duk inda suke

'Yan Najeriya sun kirkiri fasahar bin diddigin 'yan bindiga a duk inda suke

- Wani kamfani a Najeriya ya kirkiri wata fasahar bin diddiga don sanin inda 'yan bindiga suke

- Kamfanin ya bayyana cewa, fasahar za ta taimaka matuka wajen saukaka ayyukan jami'an tsaro

- Kamfanin ya kuma bayyana irin matakai da ya dauka wajen fara aikin, tare da tsammanin kammalawa

Yakin da Najeriya ke yi na rashin tsaro zai samu ci gaba nan ba da dadewa ba kasancewar kamfanin mutum-mutumi na farko a Najeriya, Robotic and Intelligence Nigeria (RAIN) ya shirya tsaf don fitar da wata fasahar bin diddigi don yaki da masu satar mutane da 'yan bindiga.

Wanda ya kirkiro kamfanin, Dr. Olusola Ayoola, ne ya bayyana kokarin samar da manhajar a garin Ibadan a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce masanan wadanda ke kan matakin kammalawa za su kara saukaka ayyukan sojojin Najeriya da sauran jami'an tsaro a kokarin da suke yi na kawo karshen satar mutane da hare-haren 'yan bindiga a kasar.

Da yake jawabi yayin karbar bakuncin Ministan Matasa da Wasanni, Mista Sunday Dare, a ofishinsa na Ibadan, Dakta Ayoola ya ce RAIN ta dukufa ne kan kirkirar fasahar sakamakon kalubalen da aka jefa ga RAIN da matasa lokacin da ministan ya ziyarci kamfanin.

KU KARANTA: Korona ta kusa fita daga Najeriya, yawan masu kamuwa da ita ya ragu

'Yan Najeriya sun kirkiri fasahar bin diddigin 'yan bindiga a duk inda suke
'Yan Najeriya sun kirkiri fasahar bin diddigin 'yan bindiga a duk inda suke Hoto: rainigeria.com
Asali: UGC

Dakta Ayoola ya fada wa ministan cewa kamfaninsu ya yi mamakin ziyarar bazata da ministan ya kawo musu a ofishinsu a watan Agustan shekarar da ta gabata don haka ya dauki kalubalen da ya jefa masu da gaske kuma suka nemi goyon baya don kirkirar manhajar ta kirkira.

Ya kuma shaida cewa, kamfanin ya nemi tallafin zakakuran masu fasaha a duniya don cimma wannan buri.

Babban Jami'in na RAIN ya bayyana cewa za a kaddamar da fasahar bin diddigin tare da sauran ayyukan kamfanin nan ba da jimawa ba, tare da tabbatar da daukar matakan da suka dace.

Hakazalika ya bayyana manufar hakan daidai da abinda minsitan ke shawartar matasan Najeriya su mai da hankali akai.

RAIN, a cewar Dr. Olusola ya damu matuka kuma ya himmatu ga ci gaba ta “hanyoyin AI, tushen ilimin kere kere da kayan yaki don yaki da aikata laifuka a Najeriya tun daga watan Agusta wanda Ministan Ci gaban Matasa ba ya da kwarin gwiwa akai"

KU KARANTA: Malaye: Ya kamata Buhari ya mika mulki dungurugum ga Osinbajo kan tafiya Landan

A wani labarin, Najeriya ta yi fiye da fitar da danyen mai kadai da wasu kayayyakin amfanin gona a shekarar 2020, ba tare da wani abin a zo a gani ba a bangaren fasahar zamani, Premium Times ta ruwaito.

A matsayinta na kasa mai dogaro da shigo da kayayyaki, kasar ta yi shekara da shekaru tana kokarin samar da kudaden shiga ta kasashen waje da kuma habaka darajar Naira, kasar na kuma fama da gibin cinikayya da ake samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel