Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tashi, ya tafi kasar Ingila

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tashi, ya tafi kasar Ingila

Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga tashar jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja domin zuwa kasar Birtaniya.

Hadimin Buhari kan gidajen talabijin da rediyo, Buhari Sallau, ya bayyana hakan da misalin karfe 3 na rana.

A cewarsa, Buhari zai gana da Likitansa don duba lafiyarsa kamar yadda ya saba.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tashi, ya tafi kasar Ingila
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tashi, ya tafi kasar Ingila Credit: Presidency
Asali: Twitter

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya fara zuwa duba lafiyarsa Landan tun kafin ya zama shugaban kasan Najeriya a 2015.

Shehu ya bayyana hakan ranar Talata yayinda yake hira da manema labarai lokacin da jirgin Buhari ya tashi daga tashar jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja.

Yace, "Shugaban kasa yana kokarin amfani da hutun bikin Easter ne. Lokacin da kowa ke hutu ne... Saboda haka zai yi amfani da lokacin wajen duba lafiyarsa."

"Wannan abu ne wanda ya dade yana yi shekara da shekaru tun kafin ya hau mulki. Duk shekara yana ganawa da Likitocinsa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel