Gwamnatin tarayya ta bada hutu ranar Juma'a da Litinin don murnar Easter

Gwamnatin tarayya ta bada hutu ranar Juma'a da Litinin don murnar Easter

- An sanar da ranar Juma'a da Litnin matsayin ranakun hutun Easter

- Ma'aikatar harkokin cikin gida ke da hakkin sanar da ranakun hutu a Najeriya

- Mabiya addinin Kirista ke bikin Easter a kowace shekara

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Juma'a, 2 ga Afrilu da Litnin 5 ga Afrilu 2021, matsayin ranar hutu don murnar bikin Ista na bana.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a jawabin da diraktan yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar, Mohammed Manga, ya saki ranar Talata.

Ya yi kira ga mabiya addini Kirista su kwaikwayi dabi'un Yesu Almasihu na soyayya da hakuri.

Aregbesola ya yi kira da Kirista su yi amfani da bikin bana wajen yiwa kasa addu'an zaman lafiya, hadin kai da cigaban.

Ogbeni Rauf Aregbesola ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen dakile yan bindiga da masu garkuwa da mutanen da suka addabi kasar.

"Lamarin tsaro matsalar kowa ne, saboda haka ina kira ga dukkan yan Najeriya a gida da waje....su bada goyon baya ga hukumomin tsaro domin samun zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiya," cewar Aregbesola.

DUBA NAN: Mahaifin daya daga cikin daliban Afaka ya mutu sakamakon bugun zuciya

Gwamnatin tarayya ta bada hutu ranar Juma'a da Litinin don murnar Easter
Gwamnatin tarayya ta bada hutu ranar Juma'a da Litinin don murnar Easter Credit: @raufaregbesola
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya tashi, ya tafi kasar Ingila

A bangare guda, shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya fito ya yi magana bayan Bola Tinubu ya bada shawarwarin magance matsalolin da ake fama da su.

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi kira ga gwamnatin Muhammadu Buhari ta duba shawarwarin da Bola Ahmed Tinubu ya bada, sannan kuma ta yi aiki da su.

Jaridar Daily Trust ta ce Femi Gbajabiamila ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa, Lanre Lasisi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel