Ina shirin mayar da rundunar sojin Najeriya mai matukar karfin iko, Attahiru

Ina shirin mayar da rundunar sojin Najeriya mai matukar karfin iko, Attahiru

- Shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya, Ibrahim Attahiru, ya sanar da cewa yana shirin mayar da rundunar mai karfin iko

- Kamar yadda ya bayyana, ana cigaba da shirya tsare-tsaren da za su tabbatar da rundunar na iya tunkarar kowanne kalubale

- Shugaban ya sanar da cewa ya amince da siyan bangarorin kayan aiki tare da gyaransu da gaggawa

Ibrahim Attahiru, shugaban rundunar sojin Najeriya ya tabbatar da cewa rundunar za ta zama gawurtacciya da za ta dinga shawo kan kalubalen tsaro a kasar nan.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, ya sanar da hakan ne yayin taron watanni uku na farkon shekara na rundunar da aka yi a ranar Litinin a Abuja.

A wata takarda da Mohammed Yerima, kakakin rundunar yasa hannun, Attahiru yace sabon salon tsaron da za su mayar da hankali shine gyaran rundunar ta kowanne fanni a kasar nan ta yadda za su iya tunkarar kowanne kalubale.

KU KARANTA: Gagarumar gobara ta lashe kasuwar doya ta Namu dake Filato

Ina shirin mayar da rundunar sojin Najeriya mai matukar karfin iko, Attahiru
Ina shirin mayar da rundunar sojin Najeriya mai matukar karfin iko, Attahiru. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

KU KARANTA: Bayan musayar wuta, 'yan sanda sun ceci mutum 5 da aka yi yunkurin garkuwa dasu a Kaduna

"Kamar yadda umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana da kuma burina na gyaran rundunar soji, na hango tabbatar da runduna mai kwarewa da kuma shawo kan kowanne kalubale," yace.

"A yanzu da muke magana, nan babu dadewa sako sabbin tsare-tsare da zasu habaka wannan ayyukan. Ana cigaba da kokarin kawar da kalubalen abubuwa masu fashewa wanda ya zama babbar matsala ga dakarun da ayyukan Operation Lafiya Dole.

“Na amince da siyan bangarorin kayan aiki da suka lalace kuma a gyara su da gaggawa. Ina tabbatar muku da cewa na shirya sake habaka dabarun yaki, kwarin guiwa da karsashin dakarun."

A watan Janairun 2021 ne Attahiru ya dasa daga inda Buratai ya tsaya na shugabancin rundunar sojin kasan Najeriya.

A wani labari na daban, an samu wata ƴar hayaniya a cikin jirgin sama na tashar jirgin Sam Mbakwe dake Owerri a ranar Lahadi tsakanin tsohon basarake, Eze Cletus Ilomuanya na jihar Imo da tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha.

Ganau sun ce Ilomuanya yana zaune hankali kwance kafin isowar Okorocha, The Nation ta wallafa.

Zuwansa ke da wuya yayi gaggawar miƙewa don rafka masa sandar da yake tafiya da ita cikin hanzari da harzuƙa.

Source: Legit.ng

Online view pixel