Korona ta kusa fita daga Najeriya, yawan masu kamuwa da ita ya ragu

Korona ta kusa fita daga Najeriya, yawan masu kamuwa da ita ya ragu

- Hukumar NCDC ta bayyana adadin mutanen da suka kamu da Korona a fadin Najeriya ranar Litinin

- Rahoton na NCDC ya nuna yadda adadin ya sauka matuka, mai nuna fitar cutar daga Najeriya

- Adadin bai kai mutum 50, hakazalika adadin mutuwa ya sauka sosai ba kamar kwanakin baya ba

Hukumar NCDC ta ruwaito cewa, mutane 48 ne kadai suka kamu da cutar ta Korona daga jihohi 8 a ranar Litinin, wata alama kuma da ke nuna cewa mai yiwuwa kwayar cutar na neman fita daga Nijeriya, PM News ta ruwaito.

Sabanin haka an bada rahoton kamuwar mutane sama da 104 a ranar Lahadi.

Daga cikin sabbin wadanda suka kamu 48, Legas tana da 13 sai kuma Kaduna mai mutum 7.

Har ila yau, Nasarawa ta bayar da rahoton kamuwar mutane bakwai, Kano 6, Kwara 5, Ondo 4, Akwa Ibom 3 sai kuma Osun 3.

KU KARANTA: Jihar Kano ta fi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya, in ji Tinubu

Korona ta kusa fita daga a Najeriya, yawan masu kamuwa da ita ya ragu
Korona ta kusa fita daga a Najeriya, yawan masu kamuwa da ita ya ragu Hoto: webmd.com
Asali: UGC

Ya zuwa yanzu, an tabbatar da wadanda suka kamu da cutar sun kai 162,641, daga cikin samfura 1,767,694 da aka gwada.

Adadin wadanda aka sallamar ya kai 150,466, yayin da wadanda har yanzu suke killace suka kai kimanin 10, 126.

An bada rahoton mutuwar mutum daya tak, a rahoton na ranar Litinin, sabanin bakwai a ranar Lahadi.

A cewar NCDC, adadin wadanda suka mutu yanzu ya kai 2,049.

KU KARANTA: Marwa da wasu jami'an NDLEA sunyi gwajin ba-zata na shan miyagun kwayoyi

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta tura Rundunar Taimakon Gaggawa zuwa Jihar Kano don gano abin da ke boye na rashin lafiya tare da kula da wadanda suka kamu a cikin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Darakta-Janar na Cibiyar hana yaduwar Cututtuka ta Najeriya, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Litinin a taron hadin gwiwa na kasa da aka yi game da Kwamitin Shugaban kasa kan Korona.

Rahotanni sun ce mutane hudu sun mutu tare da wasu sama da 200 da suka kamu da wannan bakuwar cutar da aka tabbatar a kananan hukumomi 13, ciki har da kananan hukumomi takwas na birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel