Gwamna Ganduje: Wajibi ne 'yan Najeriya su koma ga Allah

Gwamna Ganduje: Wajibi ne 'yan Najeriya su koma ga Allah

- Gwamna Ganduje na jhar Kano ya shawarci 'yan Najeriya da su koma ga Allah

- Ganduje ya yi wannan kira ne a wani taron tunawa da ranar haihuwar Bola Tinubu

- Ya kuma kirayi 'yan Najeriya da su hada kai don kawo ci gaba da habaka darajar Najeriya

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a ranar Litinin ya ce dangane da batun hadewar kasa, dole ne duk ‘yan Najeriya su koma ga Allah.

Ganduje ya bayyana haka ne a jawabinsa na maraba a taro na 12 na zagayowar ranar haihuwar Bola Tinubu da ya gudana a jihar Kano.

Taron tattaunawar, wanda aka shirya don bikin cika shekara 69 na Tinubu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, an masa taken: “Hadin kan mu, arzikin mu: Wajibi ne ga hadin kan kasa don girma da ci gaba”.

Ganduje ya yarda cewa matakin hadin kan Najeriya a halin yanzu yana cikin wani mawuyacin hali, yana mai cewa idan ba a yi wani abu ba don sauya kanun labarin, to lallai kasar na kusa da durkushewa kasa.

KU KARANTA: Ku cire mu a jerin masu son ballewa daga Najeriya, jihohin Kudu ga masu son kafa Biafra

Gwamna Ganduje: Wajibi ne 'yan Najeriya su koma ga Allah
Gwamna Ganduje: Wajibi ne 'yan Najeriya su koma ga Allah Hoto: s.rfi.fr
Asali: UGC

"Dangane da batun hadewar kasa, duk 'yan Najeriya dole ne su koma ga Allah," in ji shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan shi ne karo na farko da za a gudanar da taron a wajen Legas da Abuja tun lokacin da aka fara shi sama da shekara goma da suka gabata.

Manya irin su Shugaba Muhammadu Buhari, Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo da Shugaban kasar Laberiya, George Weah, sun halarci taron ta manhajar Zoom.

Osinbajo ya ce rashin yanayi mai kyau ne ya sa bai halarci taron a zahiri ba.

An yi hazo sosai a kewayen jihar Kano tun ranar Lahadi da mutum ba zai iya hango abu ba idan ya kai nisan mita biyar.

KU KARANTA: Mazauna wani yankin Abuja sun fara barin gidajensu saboda sace mutane

A wani labarin, Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya isa jihar Kano duk da adawar da ake nunawa kan gudanar da bikin ranar haihuwarsa a jihar.

Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa (AYCF) ta nemi Gwamna Abdullahi Ganduje da kar ya karbi bakuncin gudanar da bikin ranar haihuwar ta Tinubu a jihar.

Amma a ranar Lahadi, Ganduje ya raka Shugaban Jam’iyyar ta APC na kasa zuwa fadar mai martaba Sarkin Kano, inda ya yi masa mubaya’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel