Ku cire mu a jerin masu son ballewa daga Najeriya, jihohin Kudu ga masu son kafa Biafra

Ku cire mu a jerin masu son ballewa daga Najeriya, jihohin Kudu ga masu son kafa Biafra

- Kungiyar BRAC a kudu maso kudu ta bayyana cewa ba ta goyon bayan ballewa daga Najeriya

- Kungiyar ta bayyana bata tare da haramtacciyar kungiyar nan ta fafutukar kafa kasar Biafra

- Kodinetan kungiyar ta BRAC ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi a wani taro a birnin Abuja

Kungiyar 'yan asalin yankunan gabar teku na Bayelsa, Ribas, Akwa Ibom da Kuros Riba (BRAC) sun ce ba sa goyon bayan yunkurin neman ballewa daga Najeriya.

Sun kuma ce ba sa cikin ayyukan haramtacciyar kungiyar nan ta fafutukar 'yanta 'yan asalin Biafra.

Kodineta na BRAC, Doris McDaniels, ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi.

KU KARANTA: Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai taba alkawarin mai da Naira daidai da dala ba

Ku cire mu a jerin masu son ballewa daga Najeriya, jihohin Kudu ga masu son kafa Biafra
Ku cire mu a jerin masu son ballewa daga Najeriya, jihohin Kudu ga masu son kafa Biafra Hoto: naijiant.com
Source: UGC

Doris, ta bayyana alakar yankunan da gabar tekun da ya hada kabilu marasa rinjaye na tsohuwar yankin gabashin Najeriya wanda ya raba yankunan BRAC da na Biafra.

Daily Trust ta ruwaito tana cewa, “Bari na fada karara cewa duk da cewa BRAC ba ta da niyyar ballewa daga yankin Kudu-maso-kudu, amma mambobin kungiyar ba su cimma wata nasara ba a karkashin inuwar yankin Neja Delta.

"Babu wani ajanda gama gari da za mu dogara da shi, don tsara ci gaban yanzu da kuma nan gaba ga mutanenmu da yankin gabar teku."

KU KARANTA: Ci gaba: Tambuwal ya gwada mota kirar Najeriya mai aiki da wutan lantarki

A wani labarin daban, Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, ya ce wasu mutane kalilan ba su isa su iya shelar kafa "kasar Yarbawa" ba, ba tare da yin la’akari da babban muradin yankin kudu maso yamma ba, The Cable ta rahoto.

Sunday Adeyemo, wani shugaban matasa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ayyana Yarbawa a matsayin wata kasa ta daban kuma ya bukaci ballewar jihohin kudu maso yamma daga Najeriya.

Da yake tsokaci kan sanarwar a ranar Litinin, Akeredolu ya ce mutanen Ondo sun zabi ci gaba da zama a Najeriya, ya kara da cewa masu yada kafuwar Jamhuriyyar Oduduwa 'yan siyasa ne wadanda suka rasa madafun iko.

Source: Legit

Online view pixel