Mazauna wani yankin Abuja sun fara barin gidajensu saboda sace mutane

Mazauna wani yankin Abuja sun fara barin gidajensu saboda sace mutane

- Mazauna wani yankin babban birnin tarayya sun fara tattara kayansu suna barin garin

- Wannan ya biyo bayan yawaitar hare-hare a yankunansu dake cikin babban birnin tarayya

- Mazaunan sun koka kan yadda 'yan bindiga ke zuwa suna sace mutane tare da kashe wasu

Biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane a karamar hukumar Abaji da ke Babban Birnin Tarayya (FCT), yawancin mazauna garin sun bar gidajensu.

Daily Trust ta ruwaito yadda masu satar mutane suka kai hare-hare da yawa a yankin a cikin makonnin da suka gabata.

Mazauna yankin Anguwar Hausawa da Kekeshi ne suka fi fama da wannan matsalar.

Duk da cewa ‘yan sanda da mambobin kungiyar 'yan banga a yankin sun dakile yunkurin sace mutane daban-daban har sau uku, inda aka kashe biyu daga cikin masu garkuwar, ’yan bindigar suna ci gaba da zuwa yankin.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamna ya Ganduje ya raka Bola Tinubu zuwa fadar Sarkin

Mazauna wani yankin Abuja sun fara barin gidajensu saboda sace mutane
Mazauna wani yankin Abuja sun fara barin gidajensu saboda sace mutane Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Bayan sace wani babban ma’aikacin gwamnati a ranar Alhamis, ‘yan bindigar sun kai farmaki wani yankin Fulani da ke Kekeshi, shi ma a Abaji.

Bayan afkuwar haka, lamarin ya tilastawa ma'aikatan gwamnati da suka yi ritaya da wasu 'yan siyasa barin wurin.

Wani mazaunin Anguwar Hausawa, Ibrahim Saleh, ya ce ya yanke shawarar dauke iyalansa ne zuwa garin Abaji saboda tsoron kada a sace su.

Wata malama mai suna Misis Christiana ta ce hare-haren na ranar Alhamis din da ta gabata sun tilasta mata yin kaura daga yankin.

“Duk da cewa, an kai harin a manyan gidajen ma’aikata, karar bindigoginsu a wannan daren kadai na iya haifar da hawan jini. Saboda haka, sai na sake wuri," inji ta.

Wani mazaunin yankin, Edward Musa, wanda shi ma ya sauya wurin zama, ya ce an tilasta masa ya kaura tare da iyalinsa ne saboda yawan hare-haren.

Ya ce ya yi hayar gida mai dakuna biyu ga iyalansa a wani wuri, duk da cewa kudin hayar gidansa bai kare ba.

Wani ma'aikacin gwamnati da ya yi ritaya, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ba zai iya jurewa da hare-haren ba, saboda haka, ya yanke shawarar barin yankin.

"Bara-baran nan nayi ritaya, kuma na fahimci cewa tare da yadda masu satar mutane ke kai hari ga mazauna, ba aminci gare ni da iyalina ba," in ji shi.

Don jin ta bakin rundunar 'yan sanda game da matakan da take dauka, an tuntubi kakakin rundunar babban birnin tarayya, ASP Maryam Yusuf ta wayar salula; sai dai bata masa wayar ba kuma bata amsa sakon tes ba.

KU KARANTA: Buhari ya bukaci shugabanni da su zama nagari abin koyi ga al'umma

A wani labarin daban, Wadanda suka yi garkuwa da wasu malaman makarantar firamare ta UBE a Rama da ke karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna, sun nemi a ba su Naira miliyan 15 kudin fansa kafin su saki malaman.

‘Yan bindigan a ranar Litinin, 15 ga watan Maris, 2021, suka afkawa makarantar ta UBE suka yi awon gaba da malamai uku da yara maza uku daga wani ajin firamare, jim kadan bayan taron safe na makarantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel