'Yan sanda Sun yi ram da wani mutumi da ake zargi da hannu wajen sace Basarake a Jihar Rivers
- Rundunar 'yan sandan jihar Rivers sun samu nasarar cafke wani mutumi da ake zargin yana da hannu a sace wani Basaraken jihar Rivers
- A cewar mai magana da yawun yan Sandan jihar, a binciken da suka yi ne suka gano wasu daga cikin tufafin sarkin kuma suka kama wanda ake zargin.
- Wanda daga baya shi mutumin da ake zargi ne ya yi musu jagora har zuwa dajin da aka ɓoye basaraken suka kuɓutar dashi
Rundunar yan sanda a jihar Rivers ta kama wani mutumi mai suna Wariboko Basoene, wanda ake zargin yana da hannu a sace wani Basarake.
Mai magana da yawun rundunar, Mr Nnamdi Omoni, ya bayyana haka ranar Lahadi ya yin da yake tabbatar da kuɓutar da Basaraken, kamar yadda Channnesl TV ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Ku cire mu a jerin masu son ballewa daga Najeriya, jihohin Kudu ga masu son kafa Biafra
An dai sace Sarkin Ikuru dake karamar hukumar Andoni, jihar Rivers, Aaron Miller ne a ranar 21 ga watan Fabrairu a cikin garinsa na Ikuru.
Bayan faruwar lamarin, hukumar yan sanda ta nutsa bincike da neman basaraken wanda garin wannan aikin ne suka samu wasu daga cikin kayan sarkin kuma aka kama wanda ake zargi.
Mai magana da yawun yan sandan ya ƙara da cewa:
"Ya yin da suke bincike, wanda ake zargi ya yi bayanin daya kamata wanda daga ƙarshe shine ya yi ma jami'an mu jagora har zuwa dajin Abissa, inda aka kuɓutar da Basaraken."
KARANTA ANAN: Jam'iyyar APC Ba Za Ta Dawo Mulki Ba a Shekarar 2023, In Ji SDP
A bayanin mai magana da yawun hukumar ya ce basaraken ya kuɓuta daga hannun su ranar Asabar, makwanni biyar bayan kama shi.
Ya kuma ƙara bayyana cewa, nasarar kuɓutar da basaraken sakamako ne na aikin haɗin guiwa da hukumar yan sanda suka yi da sojojin sama.
Ya ce dukkan rundunonin biyu sun yi aiki ba kama hannun yaro da taimakon masu fasahar zamani wajen gano sawun yan bindigan.
A wani labarin kuma Mazauna wani yankin Abuja sun fara barin gidajensu saboda sace mutane
Biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane a karamar hukumar Abaji da ke Babban Birnin Tarayya (FCT), yawancin mazauna garin sun bar gidajensu.
Mazaunan sun koka kan yadda 'yan bindiga ke zuwa suna sace mutane tare da kashe wasu.
Asali: Legit.ng