Jam'iyyar APC Ba Za Ta Dawo Mulki Ba a Shekarar 2023, In Ji SDP

Jam'iyyar APC Ba Za Ta Dawo Mulki Ba a Shekarar 2023, In Ji SDP

- Jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, ta ce jam'iyyar APC ba za ta zarce ba a 2023

- Sakataren jam'iyyar na kasa, Alfa Mohammed ne ya fadi hakan yayin martani kan kalaman Shugaban riko na APC, Mai Mala Buni

- Mohammed ya ce APC ta jefa Nigeria cikin mawuyacin hali don haka ya zama dole a hada hannu a tabbatar bata cigaba da mulki ba

Jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, ta yi addu'ar cewa kada Allah ya bawa jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ikon cigaba da rike mulkin kasa bayan babban zaben 2023, The Punch ta ruwaito.

Jam'iyyar hammayar ta ce fatan yan Nigeria shine mulkin shugaba Muhammadu Buhari ya zama karshen jam'iyyar APC a kasar.

Jam'iyyar APC Ba Za Ta Dawo Mulki Ba Bayan 2023, In Ji SDP
Jam'iyyar APC Ba Za Ta Dawo Mulki Ba Bayan 2023, In Ji SDP. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Nasara Daga Allah: Bidiyon Makaman Da Sojoji Suka Ƙwato Bayan Kashe Ƴan Boko Haram 48 a Borno

A hirar da ya yi da wakilin majiyar Legit.ng a ranar Juma'a, Alfa Mohammed, Sakataren SDP na kasa, ya yi kira da sauran jam'iyyu masu irin tunaninsa su hada hannu wuri guda don kawar da APC a babban zaben da ke tafe a 2023.

Shugaban kwamitin riko na kasa na APC, Mai Mala Buni, a ranar Talata ya ce jam'iyyar mai mulki na nufin cigaba da rike mulki na tsawon shekaru 32 nan gaba.

A martaninsa kan shirin da APC ke yi don cigaba da mulki har shekaru 32 nan gaba, Mohammed ya ce, "Da farko, Allah kada ya bawa APC nasara a zaben da ke tafe.

DUBA WANNAN: Bidiyon Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Arewa House Ya Janyo Maganganu

"Idan kasa ta tsinci kanta cikin rashin sa'a na samun gwamnati wadda ba ta iya mulki ba kamar APC a yanzu, yana da muhimmanci yan kasar su hada kai domin ganin gwamnatin ba ta cigaba da mulki ba."

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel