2023: Kan Gwamonin PDP ya rabu 2 bayan shawarar da kwamitin Gwamna Bauchi ya bada
- Ana ta samun sabanin ra’ayi a game da yankin da za a ba tikitin takara a PDP a 2023
- Wasu Gwamnoni ba su goyon bayan shawarar da kwamitin Bala Mohammed ya bada
- Gwamna Bala Mohammed ya bukaci ayi watsi da tsarin kama-kama a zabe mai zuwa
Gwamnonin da ke rike da jihohin PDP su na karo da juna a game da rahoton da kwamitin gwamna Bala Mohammed da ya duba abin da ya faru a zaben 2019 ta fitar.
Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar 29 ga watan Maris, 2021, cewa shawarar da kwamitin ya bada na yin watsi da tsarin karba-karba ya raba kan gidan PDP.
Wasu gwamnonin su na ganin akwai abin da gwamna Bala Mohammed yake nufi tun farko da kwamitinsa ta bada shawarar a bar kofar neman takarar 2023 a bude.
KU KARANTA: Buhari, Lawan, Omo Agege sun koda Tinubu bayan cika 69
Inda wannan shawara ta fi tada kura a reshen jam’iyyar hamayyar shi ne yankin kudu maso gabas, inda ake da ra'ayin cewa ya kamata mulki ya bar yankin Arewa.
Surutan da aka fito ana yi ya sa dole sakataren yada labaran PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya fitar da jawabi, ya na cewa ba a dauki shawarar kwamitin ba tukuna.
Wata majiya ta shaida mana cewa: “Mafi yawan gwamnoni ba su ji dadin matsayar da gwamnan jihar Bauchi ya dauka na fitar da rahoton kwamitin na sa a fili ba."
“Dalili shi ne, har yanzu ana tattaunawa kan wannan batu tsakanin gwamnoni, kafin a fitar da rahoton.”
KU KARANTA: Cancantar ‘dan takara ba yankinsa ba zai yi aiki a zaben 2023
“Gwamnonin jihohi su na da sabanin fahimta a game da abin da ya kamata jam’iyya ta yi game da tsarin kama-kama wajen bada tikitin takarar shugaban kasa a 2023.”
“Har wasu daga cikin ‘yan kwamitinsa, ba su amince da shawarar Bala Mohammed ba.” Hakan ya sa ake gani gwamnan ya yi azarbabin fitar da rahoton aikin da ya yi.
“Wani gwamna daga yankin Kudu maso gabas ya fito ya na zargin gwamna Mohammed da shugaban PDP, Prince Secondus da kokarin fifita Atiku a zaben 2023.”
Kwanaki wata kungiya ta ILDF ta soki kwamitin Bala Mohammed, ta ce ana shiri ta bayan-gida a jam'iyyar PDP domin a sake ba ‘Dan Arewa takara a zabe mai zuwa.
Kungiyar Igbo Leadership Development Foundation ta ce akwai wani lauje cikin nadi a PDP bayan ganin shawarwarin da kwamitin gwamnan Bauchi ya ba jam'iyya.
Asali: Legit.ng