Lokaci ya yi: Mai ba Gwamna Masari shawara ya yanke jiki ya mutu ana tsakiyar biki

Lokaci ya yi: Mai ba Gwamna Masari shawara ya yanke jiki ya mutu ana tsakiyar biki

- Wani mai ba Gwamnan jihar Katsina shawara kan harkar tsaro ya rasu

- Alhaji Rabe Ibrahim Jibia ya yanke jiki fadi ne wajen taron daurin aure

- Ko da aka tafi asibitin gidan gwamna, sai aka tabbatar da cewa ya mutu

Rahotanni sun bayyana cewa wani daga cikin masu ba gwamnan jihar Katsina shawara, Rt Hon Aminu Bello Masari, ya fadi a wurin bikin aure.

Jaridar Katsina Post ta fitar da rahoto cewa daga wannan yanke jiki ne Alhaji Rabe Ibrahim Jibia ya rasu a ranar Asabar, 27 ga watan Maris, 2021.

Marigayi Rabe Ibrahim Jibia shi ne mai ba mai girma gwamnan jihar Katsina shawara a kan harkar tsaron na abin da ya shafi shiyyar garin Daura.

KU KARANTA: Yankin Karaduwa za ta samu Jami’ar Tarayya a garin Funtua

Wannan Bawan Allah ya fadi ne a lokacin da ake daura auren ‘diyar wani abokin aikinsa, Alhaji Ibrahim Katsina a unguwar GRA, Katsina.

Shi ma mahaifiyar wannan Amarya, Alhaji Ibrahim Katsina ya na cikin masu ba gwamna Aminu Bello Masari shawara a kan sha’anin tsaro.

Ba a dade da gwamnan Katsina ya nada Rabe Ibrahim Jibia a matsayin mai ba shi shawara ba, sai rai ya yi halinsa, shi kuwa ya ce ga garinku nan.

KU KARANTA: Yadda za a bi a shawo kan matsalar zaman kashe wando - Atiku

Lokaci ya yi: Mai ba Gwamna Masari shawara ya yanke jiki ya mutu ana tsakiyar biki
Gwamnan Katsina Aminu Masari Hoto: @GovernorMasari
Asali: Twitter

Da aka ruga da Marigayi Rabe Ibrahim Jibia zuwa asibitin gidan gwamnati bayan ya yanke jiki, sai likitoci su ka tabbatar da cewa ya riga ya cika.

Jaridar ta ce marigayin tsohon jami’in hukumar DSS masu tsaro ne leken asiri da fararen kaya ne bayan ya yi ritaya ne aka ba shi mukami a gida.

Tuni aka yi masa sallar jana’iza, aka bizne, shi a garin Katsina kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

A makon da ya gabata kun ji cewa Sanata Bode Olowoporoku, wani tsohon Ministan jamhuriyya ta biyu kuma tsohon Sanatan Najeriya ya rasu.

An bada sanarwar cewa Dr. Bode Olowoporoku ya kwanta dama a gidansa. Marigayin ya yi aiki da gwamnatocin Shehu Shagari da Olusegun Obasanjo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng