Dole a saka Tinibu a cikin Jagororin da suka gina Nigeria, Inji gwamnan Legas Sanwo-Olu
- Gwamnan jihar Lagos, Sanwo-Olu ya bayyana cewa dole a saka jagoran APC Bola Tinibu a jerin waɗan da suka bada gudummuwar su wajen gina Najeriya
- Gwamnan ya ce, tsohon gwamnan na daga cikin mutanen da za'a bada labarin su matuƙar za'a faɗi labarin Najeriya.
- Sanwo-Olu ya taya tsohon gwamnan murnar cika shekru 69 a duniya amadadin sa da matarsa da kuma al'ummar jihar Legos baki ɗaya.
Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya ce jigon jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya bada gudummuwa mai yawa wajen gina Najeria.
KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Bidiyo da Hotunan Gobarar Da Ta Tashi Kusa Da Masallacin Annabi a Madina
A wani jawabi na taya murna a bikin zagayowar haihuwar Tinubu, Sanwo Olu yace demokaraɗiyyar ƙasar nan ba zata cika ba sai an saka Tinibu.
Ya yin da yake bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai hangen nesa kuma abokin shawara nagari dake da ilimi a fannoni da dama na rayuwar al'umma, gwamnan ya ce:
"Labarin demokaraɗiyyar ƙasar Najeriya bazai cika ba matuƙar ba'a ambato sunan 'Jagoran Burgu' ba wato Bola Tinibu. Dubbannin mutane a yau suna cin gajiyar siyasar sa."
Hakanan kuma, gwamnan ya taya iyalan tsohon gwamnan murna, musamman me ɗakinsa, sanata Olerime Tinibu, abokanan sa, abokan siyasar sa,, jagororin APC da kuma mambobin APC da ke faɗin ƙasar nan bisa zagayowar haihuwar jagoran.
"A madadin mai ɗakina da kuma al'ummar jihar Lagos da mambomin jam'iyyar mu ta APC, ina ta ya jagoran mu muranar cika shekara 69 a duniya."
KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Shugaban PDP da Manyan Ƴan Jam'iyyar Sun Dunguma Sun Koma APC a Ebonyi
"Kamar yadda kake tunkarar wata sabuwar rayuwa, ina fatan Allah ya tsare ka a dukkan lamurran ka kuma ya baka nasara a ayyukan alkairin da kake ma ƙasar mu da al'ummar ta." inji gwamnan.
A wani labarin kuma 'Yan fashin da suka sace mambobin RCCG sun nemi a biya 50 Miliyan
Yan fashin da suka sace mambobin ƙungiyar addinin kirista RCCG a Kaduna sun nemi a biya su 50 miliyan kuɗin fansa kafin su sake su
Mai magana da yawun RCCG a jihar Kaduna Alao Joseph ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan masu garkuwan sun tuntuɓe su.
Asali: Legit.ng