'Yan fashin da suka sace mambobin RCCG sun nemi a biya 50 Miliyan

'Yan fashin da suka sace mambobin RCCG sun nemi a biya 50 Miliyan

-Yan fashin da suka sace mambobin ƙungiyar addinin kirista RCCG a Kaduna sun nemi a biya su 50 miliyan kuɗin fansa kafin su sake su

- Mai magana da yawun RCCG a jihar Kaduna Alao Joseph ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan masu garkuwan sun tuntuɓe su.

- A daren jumu'a ne a ka sace mambobin kuma hukumar yan sanda ta tabbatar da cewa tana gudanar da bincike don ƙuɓutar da mutanen da aka sace.

Waɗan da suka sace mambobin ƙungiƴar addinin kirista RCCG a jihar Kaduna sun nemi a biya 50 miliyan kuɗin fansa kafin su sake su.

KARANTA ANAN: Shugabannin majalisun dokokin Arewa mao yamma sun yi alkawarin goyon bayan Tinubu a 2023

Mai magana da yawun majami'ar RCCG Kaduna, Alao Joseph ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Mr. Joseph ya faɗa ma Channels TV cewa, yan fashi sun sace mambabin ne da misalin ƙarfe 7 na daren ranar jumu'a a kan hanyar Kachia.

Ya kuma ƙara da cewa yan fashin sun yi awon gaba da mambobin zuwa wani wuri da ba'a sani ba, sannan suka bar motar mutanen nan kan hanya.

Mr. Joseph ya ce mun faɗa ma hukumomin tsaro abinda ya faru kuma muna fatan zasu taimaka wajen kuɓutar da waɗan da aka sace.

'Yan fashin da suka sace mambobin RCCG sun nemi a biya 50 Miliyan
'Yan fashin da suka sace mambobin RCCG sun nemi a biya 50 Miliyan Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Hukumar yan sanda a jihar Kaduna sun tabbatar da ɓacewar mambobi takwas na RCCG a ranar Jumu'a da daddare.

KARANTA ANAN: Kwana 2 bayan gyara wutan Maiduguri, yan Boko Haram sun sake lalatawa

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Mohammed Jalige, a sa'ilin da ya tabbatar da faruwar lamarin ga Channels TV yace:

"Hukumar yan sanda tana aiki tare da shuwagabannin majami'ar RCCG din don tabbatar da mutane nawa ne aka sace."

Ya kuma ƙara da cewa jami'an 'yan sanda sun ƙaddamar da sintiri na musamman don zaƙulo waɗan da suka aikata haka da kuma kuɓutar da waɗan ada aka sace a raye.

A wani labarin kuma Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya aikewa shugaba Buhari goron gayyata

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya gayyaci shugaba Muhammadu Buhari taron sauyin yanayi da za'a gudanar ta yanar gizo a watan Afrilu.

An gayyaci Buhari ne tare da wasu shugabannin kasashe 39 a duniya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel