Matsalar Tsaro: Gwamnatin jihar Neja ta sanar da ranar bude dukkan makarantunta

Matsalar Tsaro: Gwamnatin jihar Neja ta sanar da ranar bude dukkan makarantunta

- Gwamnatin jihar Neja ta bayyana ranar da za'a sake buɗe makarantun dake jihar bayan sati biyu suna kulle

- Kwamishinar ilimin jihar ce ta bayyana haka a wani jawabi da ta saka ma hannu bayan taron masu ruwa da tsaki a fannin ilimin jihar

- Ta ce za'a koma makarantar ne mataki-mataki, kuma za'a ƙara jami'an tsaro a garuruwan dake da hatsari.

Gwamnatin jihar Neja ta bayyana ranar da za'a sake buɗe makarantun sakandire a faɗin jihar, sati biyu bayan kullesu, jaridar Punch ra ruwaito.

Gwamnatin ta kulle makarantun ne a ƙoƙarin ta na kare ɗaliban jihar bayan faruwa lamarin da ya sa a ka sace ɗalibai da ma'aikata a makarantar sakandiren Kagara.

KARANTA ANAN: Babu dan siyasa na hakika da zai yi watsi da damar zama shugaban kasa – Fayemi

Gwamnatin jihar ta yanke hukuncin komawa makarantun ne ranar Litinin bayan ma'aikatar ilimi ta yi babban taro da duk masu ruwa da tsaki a fannin ilimin jihar.

A wani jawabi da kwamishinar ilimin jihar Neja, Hajiya Hannatu Jibrin Salihu, ta saka ma hannu ta bayyana cewa za'a buɗe makarantun ne a mataki-mataki.

Jawabin yace "Dukkan makarantun jeka ka dawo na bai ɗaya su buɗe makaranta a ranar Litinin 29 ga watan Maris."

"Sannan dukkan makarantun sakandiren kwana dake cikin biranen jihar za su buɗe makarantun su ranar shida ga watan Afrilu."

"Hakanan kuma, makaantun sakandiren kwana dake yankunan karkara su buɗe makarantun su ranar shida ga watan Afrilu,"

Matsalar Tsaro: Za'a koma makarantun sakandire a jihar Neja tun bayan Harin da aka kai Jangeɓe
Matsalar Tsaro: Za'a koma makarantun sakandire a jihar Neja tun bayan Harin da aka kai Jangeɓe Hoto: @NigerStateNG
Source: Twitter

"Sannan kuma , sauran makarantun sakandiren jeka ka dawo dake yankuna masu hatsari zasu cigaba da kasancewa a rufe amma za'a zaɓi wasu makarantu dake kusa a tura daliban su, za'a sanar da ran da zasu koma bayan an yi duk shirye-shiryen da ya kamata,"

KARANTA ANAN: Kawai a kasheta, Mahaifin Amaryar da Kishiyarta ta bankawa wuta ya bukaci hukuma

Gwamnatin ta ƙara da cewa ɗalibai daga yankunan da aka maida makarantun kwanan su zuwa jeka-ka-dawo, za'a mai da su makarantun kwana ko na jeka ka dawo dake kusa da garuruwansu.

Jawabin kwamishinar ya cigaba da cewa:

"An baiwa dukkan shuwagabannin sakandire abun da ya kamata na bayanin da ke ƙunshe a shirye-shiryen da aka yi, sabida haka muna fatan su yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da shuwagabannin ilimin yankin su don tabbatar da tsaro."

"Dukkan makarantun jihar, musamman waɗan da ke wajen da ke da hatsari, za'a ƙara tsaurara tsaronsu wajen samar da jami'an tsaro da zasu kula da makarantar dan jiran ko ta kwana."

Daga ƙarshe an umarci shugabannin makarantu su tabbatar da an bi dokokin kare yaɗuwar cutar COVID19.

A wani labarin kuma ‘Yan Najeriya na kashe sama da N1trn don kare kansu a duk shekara.

Cif Kenny Martins, wani jagora a Najeriya ya koka kan yadda 'yan Najeriya ke kashe kudi a tsaro.

Ya bayyana cewa, akalla ana kashe sama N1trn a duk shekara a daukar masu gadi da sauran ababen tsaro.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel