Kawai a kasheta, Mahaifin Amaryar da Kishiyarta ta bankawa wuta ya bukaci hukuma
- Mahaifin Fatima yace sam ba zai yafewa wadanda suka kashe diyarta ba
- Watanni biyu da aure, kishiya ta kashe Amaryar mijinta a jihar Neja
- Wannan abu ya janyo cece-kuce a kafafen ra'ayi da sada zumunta
Mahaifin matar da kishiya ta hallaka ta hanyar banka mata wuta ya bukaci hukumomi su tabbatar da cewa an kashe wacce aka kama da wannan laifi.
Malam Ibrahim Yayaha Sidi Na Khalifa ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da Daily Trust.
Ya ce abinda yake so kawai shine a yanke mata hukuncin da ya kamata.
Ya ce a addinin Musulunci, babu laifi idan mutumin da aka zalunta ya zabi daukar fansa saboda Al-Qur'ani ya bayyana hukuncin kisa ba tare da hakki ba.
"Ba zan taba yafe jinin diyata ba. Qur'an yace ' Mun hukunta cewa rai ga rai'.... saboda haka ina son ganin an yanke hukunci kan wadanda suka aikata wannan abin takaicin," Yace.
"Ba zan taba yafe musu ba. Ba hadari bane ko kuskure. Ki bugi diyata har lahira, sannan ki bankawa gawarta wuta, ba zan taba yafewa ba."
DUBA NAN: Rundunar Sojin Najeriya sun yi zanga-zanga kan rashin isassun makamai
Rahotanni sun kawo cewa wata mata ta lakadawa kishiyarta dukan tsiya sannan ta cinnawa gawarta wuta.
Kishiyar mai suna Fatima daga yankin Sabuwar Unguwa, garin Katsina, ta yi aure kimanin watanni biyu da suka gabata
A cewar wata majiya ta kusa da iyalan, lamarin ya afku ne a ranar Talata
"Na ji cewa matar ta je gidan Fatima tare da mutum daya ko biyu," tace
“Shakka babu ba da niyan kasheta suka yi ba, amma da suka ga cewa bata numfashi bayan sun yi mata duka, sai suka cinnawa dakinta da gawarta wuta."
Asali: Legit.ng