Babu dan siyasa na hakika da zai yi watsi da damar zama shugaban kasa – Fayemi

Babu dan siyasa na hakika da zai yi watsi da damar zama shugaban kasa – Fayemi

- Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya ce ya fi sha'awar karasa wa'adinsa bisa kyakkyawar nasara a 2022

- Sai dai, Fayemi, ya bayyana cewa kudirinsa na takarar shugaban kasa har yanzu jita-jita ne

- Shugaban NGF din ya ce duk wani dan siyasa na hakika yana son zama shugaban Najeriya

Bayan ce-ce-ku-ce daa aka shafe watanni ana yi game da kudirinsa na shugabancin kasa a 2023, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce zai tsallaka gadar idan ya isa wurin.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa gwamnan yace babu wani dan siyasa na gaske da zai yi watsi da damar zama shugaban kasar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: 2023: Dalilin da yasa muka bari tsohon Shugaban hafsan soji ya dawo cikinmu, APC ta magantu

Babu dan siyasa na hakika da zai yi watsi da damar zama shugaban kasa – Fayemi
Babu dan siyasa na hakika da zai yi watsi da damar zama shugaban kasa – Fayemi Hoto: @kfayemi
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa Fayemi ya fadi haka ne a wani shirin gidan Talabijin din Channels, wanda aka watsa shi a ranar Juma'a, 26 ga watan Maris.

Da farko dai majalisar dokokin jihar Ekiti ta lamuncewa Fayemi don ya zama Shugaban kasa.

Ya ce: “Ina dariya. Kun san dalili? Ina samun wannan tambayar koyaushe. Ban san wani dan siyasa mai hankali da zai sami damar mulkar wata kasa tare da albarkar da muke da ita duk da kalubalen muke da ita amma ya ki yi amfani da damar ba, sai dai har yanzu ba mu kai nan ba."

Gwamnan, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen rusa uwar Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, ya ki bayyana takamaiman magana kan ko zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

KU KARANTA KUMA: 2023: Tinubu ya shiga matsala yayinda matasan Arewa suka aika sakon gargadi ga Ganduje

Sai dai, Fayemi, ya ce ya maida hankali ne ga kammala wa’adinsa a watan Oktoba 2022.

Ya ci gaba da cewa:

“Ina la’akari da kammalawa da kyau a Ekiti a 2022. Ina da aiki. Gaskiya, ina godiya har abada ga mutanen Ekiti da suka ba ni dama na mulki jihar sau biyu kuma har yanzu ina da abubuwa da yawa da zan gabatar game da hakan.

“Don haka, nan gaba za ta kula da kanta. Ba ni da wata hanyar sanin abin da zai faru ta wurina, tabbacin shi ne ni gwamnan jihar Ekiti ne kuma wannan wa’adin zai kare ne a watan Oktoba na 2022. Wannan shi ne aikin da nake da shi a yanzu.”

A wani labarin, ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio, ya ce ba shi da wata alaka da baturen zaben da kotu ta jefa kurkuku kan taimakawa wajen magudin zabe.

Hakazalika Akpabio ya yi watsi da maganganun cewa baturen zaben ya taya shi da jami'yyar APC magudi a zaben.

Akpabio ya ce gaskiyan abinda ya faru shine shi aka yiwa magudi a zaben na 23 ga Febrairu, 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel