Nasara Daga Allah: Bidiyon Makaman Da Sojoji Suka Ƙwato Bayan Kashe Ƴan Boko Haram 48 a Borno

Nasara Daga Allah: Bidiyon Makaman Da Sojoji Suka Ƙwato Bayan Kashe Ƴan Boko Haram 48 a Borno

- Dakarun sojojin Nigeria sun samu gagarumin nasara kan yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno

- Sojojin, yayin hare-haren da suka kai a hanyar Askira-Chibok da Chibok-Damboa sun kashe yan ta'adda 48

- Sojojin sun kuma yi nasarar ceto mutane 11 da yan ta'addan suka sace tare da kwato bindigu da wasu makamai

Dakarun Sojojin Nigeria na Lafiya Dole sun kashe yan ta'adda masu yawa sakamakon harin kwantar bauna da suka kai musu a garin Chibok, a jihar Borno, The Cable ta ruwaito.

Mohammed Yerima, kakakin rundunar sojoji, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar ya kara da cewa sojojin sun ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su a Borno.

DUBA WANNAN: Na Bar Mijina Saboda Girman Mazakutarsa, Matar Aure ta Shaidawa Kotu

Sojoji Sun Sada Ƴan Boko Haram 48 Da Mahallacinsu, Sun Ceto Mutum 11 da aka Sace a Borno
Sojoji Sun Sada Ƴan Boko Haram 48 Da Mahallacinsu, Sun Ceto Mutum 11 da aka Sace a Borno. @ChannelsTV
Asali: UGC

Ya ce sojojin sun kai harin ne bayan samun bayannan sirri na cewa yan ta'adan da suka yi saura suna tserewa saboda ragargazar da sojojin ke musu a Dajin Sambisa.

"Dakarun sojojin Nigeria da aka tura Chibok a karkashin Operation Lafiya 28 Task Force Brigade 1 sun kashe yan ta'adda da dama a harin kwantar bauna da suka kai musu a hanyar Chibok-Damboa a jihar Borno," a cewar Yerima.

KU KARANTA: Bidiyon Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Arewa House Ya Janyo Maganganu

"Sojojin sun musu kwantar bauna, suka bude musu wuta, suka kashe guda 9 yayin da wasu da dama suka tsere da raunin bindiga. Sojojin sun kwato AK47 guda 7 sannan sun ceto mutum 3 da aka sace.

"Kazalika, a wani harin, Sojojin 28 Task Force Brigade da ke Askira sun yi nasarar kai harin kwantar bauna a hanyar Askira-Chibok sun kashe yan ta'adda 39.

"Sakamakon harin, sojojin sun ceto mutum 8 da yan ta'addan suka sace. Daya daga cikin wadanda aka ceto ya samu rauni a kafarsa yayin da ya ke hannun yan ta'addan don haka an tura shi asibitin sojoji don masa magani.

"Yayin harin, sojojin sun kwato bindigu AK 47 guda takwas da harsashi hudu da wasu kayayakin."

Ga bidiyon makaman da sojojin suka kwato a kasa:

Yerima ya kara da cewa babban hafsan sojojin kasa, Ibrahim Attahiru ya yaba da jajircewar sojojin ya bukaci su cigaba da hakan har sai sun fatattaki dukkan yan ta'adda da suka yi saura a yankin.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters

Asali: Legit.ng

Online view pixel