Ba ni ya taya ba, Ministan Buhari ya nisanta kansa daga Baturen zaben da aka jefa kurkuku kan taya APC magudi
- Kwana biyu ba'a hukuncin kotu kan baturen zabe da INEC ta shigar Kotu, Apkabio ya yi magana
- Ministan Buharin ya ce shi aka cuta a zaben kuma ba shi yayi niyyar cuta ba
- Ya tuhumi hukumar INEC da kokarin juya maganar kansa tare da daura masa laifi
Ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio, ya ce ba shi da wata alaka da baturen zaben da kotu ta jefa kurkuku kan taimakawa wajen magudin zabe.
Hakazalika Akpabio ya yi watsi da maganganun cewa baturen zaben ya taya shi da jami'yyar APC magudi a zaben.
Akpabio ya ce gaskiyan abinda ya faru shine shi aka yiwa magudi a zaben na 23 ga Febrairu, 2019.
A jawabin sakataren yada labaran Ministan, Aniete Ekong, ya saki a Abuja ranar Asabar, ya tuhumi hukumar gudanar da zabe ta kasa INEC da juya ma'anar shari'ar kotu, rahoton The Nation.
"A yunkurin da suke yi na cigaba da batawa Sanata Akpabio suna, INEC a jihar Akwa Ibom ta juya ma'anar hukuncin kotu ta yadda za'ayi tunanin Sanata Akpabio aka taya magudi," wani sashen jawabin yace.
"Alhali Sanata Akpabio aka yiwa magudi a zaben kujerar Sanatar Akwa Ibom NorthWest a zaben da akayi ranar 23 ga Febrairu, 2019."
DUBA NAN: Buhari Ya Karɓi Baƙuncin Shugaba Idriss Deby a Fadarsa ta Aso Rock
KU KARANTA: 2023: Dalilin da yasa muka bari tsohon Shugaban hafsan soji ya dawo cikinmu, APC ta magantu
Wata babbar kotu dake jihar Akwa Ibom ta yankewa wani Farfesan jami'ar UNICAL, Peter Ogban, hukuncin daurin shekaru 3 a gidan gyara hali bayan kama shi da laifin sauya sakamakon zabe.
Ogban ya kasance baturen zabe a zaben kujerar Sanatan Akwa Ibom North-West a 2019
An tuhumeshi da laifin sanar da sakamakon zaben karya a kananan hukumomi biyu - Oruk Anam and Etim Ekpo.
Asali: Legit.ng