2023: Dalilin da yasa muka bari tsohon Shugaban hafsan soji ya dawo cikinmu, APC ta magantu
- Ga jam'iyyar APC, yankin kudu maso gabashin Najeriya sna iya samun gagarumin gurbi a zaben shugaban kasa na 2023
- Jam’iyyar mai mulki ta ce wannan na daga cikin dalilin da ya sa ta karbi tsohon shugaban rundunar sojan Najeriya wanda yake haifaffen jihar Abia, Azuibike
- Mai Mala Buni ya bayyana wannan komawar ta Ihejirika a matsayin babbar nasara ga jam'iyyarsu
Shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi magana kan dalilin da yasa ta kyale tsohon shugaban hafsan soji (COAS), Azubuike Ihejirika, ya shiga cikin ta.
Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, ya bayyana cewa wannan karimcin na jam'iyya mai mulki ya kasance musamman saboda ra'ayin jihar Abia ne da kudu maso gabashin kasar baki daya, jaridar The Cable ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: 2023: Tinubu ya shiga matsala yayinda matasan Arewa suka aika sakon gargadi ga Ganduje
A cewar jaridar The Sun, Buni ya ce dawowar Ihejirika cikin jam'iyyar zai kara taimakawa jihar wajen shigo da APC ta yadda za a dama da yankin a harkar siyasa.
Shugaban APC din ya ce:
“Zuwan Janar Ihejirika zai karawa jam’iyyar tagomashi a jihar Abia da kudu maso gabas gaba daya.
“Wannan wani lokaci ne mai kyau ga jam’iyyar yayin da Janar Ihejirika da sauran 'ya’yan yankin maza da mata ke shigowa jam’iyyar don isar da yankin da kuma kawo kudu maso gabas tsakiya. Muna fatan samun karin karfi a yankin kudu maso gabas.”
KU KARANTA KUMA: Tashin hankali a Kaduna yayin da wasu 'yan fashi suka sace mambobin RCCG 8
A wani labarin, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi waiwaye kan yakin basasan da aka kwashe watanni 30 ana yi a Najeriya kuma ya yi addu'a kada Allah ya maimaitawa Najeriya irin wannan yaki.
Mai magana da yawun shugaban kasan, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya sake mai taken "Shugaba Buhari ya aika ta'ziyya ga shahidan yakin basasan Najeriya."
Najeriya, karkashin Janar Yakubu Gowon ta shiga yaki da Biyafara da suka balle karkashin jagorancin Laftanar Kanar Odumegwu Ojukwu tsakanin 6 ga Yulin 1967 da 15 ga Junairun 1970.
Asali: Legit.ng