Yana da matukar wuya a siyar da gurbataccen kaya, Baba-Ahmed ya yi wa Garba Shehu ba’a a shirin talbijin

Yana da matukar wuya a siyar da gurbataccen kaya, Baba-Ahmed ya yi wa Garba Shehu ba’a a shirin talbijin

- Kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed ya yi shagube ga mai magana da yawun Shugaba kasa, Malam Garba Shehu

- A cewar Baba-Ahmed yana matukar tausayawa Shehu saboda yana da wahala mutum ya iya sayar da gurbataccen kaya

- Ya shawarci shugaban kasa da ya yi aikinsa sannan ya daina zargin wasu kan abubuwan da yake ba daidai ba a cikin gwamnatinsa

Kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed, ya yi kakkausar suka ga Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari.

Lokacin da bayyana a shirin Sunrise Daily, na gidan Talabijin din Channels a ranar Juma'a, Baba-Ahmed ya ce yana tausayawa Shehu saboda "Yana da matukar wahala a sayar da lalataccen kaya".

Shehu, wanda shi ma bako ne a shirin, ya ce wasu mutane ba za su cimma nasara ba a yunkurinsu na durkusar da gwamnatin Buhari.

Yana da matukar wuya a siyar da gurbataccen kaya, Baba-Ahmed ya yi wa Garba Shehu ba’a a shirin talbijin
Yana da matukar wuya a siyar da gurbataccen kaya, Baba-Ahmed ya yi wa Garba Shehu ba’a a shirin talbijin Hoto: @Abubakardnk
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Hotunan babur mai doguwar kujerar da ka iya daukar mutum 8 ta haddasa cece-kuce

Yayinda yake mayar da martani ga kiraye-kirayen wasu masu son a barka kasa kamar su Sunday Igboho da Asari Dokubo, Shehu ya ce ana daukar nauyin wasu “mayaudara” don su yiwa Buhari zagon kasa, suna ganin hakan zai tilasta masa mika wuya.

A yayin shirin talabijin, Shehu ya danganta ayyukan “masu boren” ga masu adawa da gwamnati.

Amma Baba-Ahmed ya ce ainihin abin da yake so daga shugaban kasar shi ne ya yi aikinsa kuma kada ya ci gaba da zargin wasu kan abubuwan da yake ba daidai ba a cikin gwamnatinsa.

“Da farko dai, dole ne in ce ina matukar tausaya wa Malam Garba Shehu saboda yana da matukar wahala a sayar da kaya mara kyau. Yana yin aikinsa; aikinsa shi ne yi wa gwamnati gyaran fuska. Amma ‘yan Najeriya sun san yadda abubuwa suke.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Gwamnatin Najeriya za ta gina kamfanin takin zamani na dala biliyan 1.3

"Babu bukatar a sanya masu suka suna a matsayin mutanen masu daukar hankali, wadanda ke son durkusar da kasar."

A baya mun ji cewa, a ranar Juma’a, 26 ga watan Maris, 2021, fadar shugaban kasar Najeriya ta ce ba a isa ayi kasa da wannan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari ba.

Fadar shugaban kasa ta yi jawabin ne ta bakin mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Garba Shehu, lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin.

Garba Shehu ya caccaki masu fafutukar barkewa daga Najeriya, ya ce wasu mutane ne su ke goya wa wadannan bata-garin mutane masu yi wa kasar barazana.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel