Masu kiraye-kirayen a barka kasa sun yi kadan su sauke ni daga kujera kafin 2023 inji Buhari
- Fadar shugaban kasa ta tanka wadanda su ke faman kiran a raba kasa
- Garba Shehu ya ce babu wanda zai iya sauke Buhari daga kujerar mulki
- Hadimin ya ba masu wannan kira shawara su fito neman takara a 2023
A ranar Juma’a, 26 ga watan Maris, 2021, fadar shugaban kasar Najeriya ta ce ba a isa ayi kasa da wannan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari ba.
Fadar shugaban kasa ta yi jawabin ne ta bakin mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Garba Shehu, lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin.
Garba Shehu ya caccaki masu fafutukar barkewa daga Najeriya, ya ce wasu mutane ne su ke goya wa wadannan bata-garin mutane masu yi wa kasar barazana.
KU KARANTA: Abin da ya hana Shugaban kasa tsige hafsoshin tsaro - Garba Shehu
Shehu ya ce wadannan ‘yan je-ka-na-yi-ka, ba za su iya sauke shugaba Buhari daga mulki a haka ba. Hadimin ya ce har gobe akwai wadanda ke tare da gwamnatin.
Fadar shugaban kasar ta nuna wa masu wannan kira da cewa Muhammadu Buhari ya samu mulki ne hanyar zaben, don haka su kara hakuri har sai zuwa 2023.
"Masu mugun buri su dakata sai nan da shekaru biyu, su yi takarar shugaban kasa a zaben 2023."
“Ina so in tabbatar wa ‘Yan Najeriya gwamnatin Muhammadu Buhari ta na kokarin shawo kan tulin matsalolin da ke addabar kasar, musamman a harkar tsaro.”
KU KARANTA: Buhari ya kawo tasgaro wajen ceto Daliban da aka yi ram da su - Gumi
Duk da matsalar tsaro, Malam Shehu ya ce shugaban kasar ya yi nasara a bangarorin tattalin arziki, noma, da yaki da rashin gaskiya, wadanda su ne su ka kai shi ofis.
“Abin takaici ne ‘yan adawa su na amfani da wadannan abubuwa. Ina mai tabbatar maku cewa shugaban kasa ya jajirce wajen tsare kasa da kawo zaman lafiya.” Inji shi,
A halin yanzu kun san cewa akwai irinsu Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho da Banji Akintoye da su ke kiran kasar Yarbawa ta barke daga Najeriya.
Haka zaika tsohon tsageran Neja-Delta, Mujahid Asari-Dokubo ya dawo da maganar samar da Biyafara bayan ya kafa kungiyar Biafra de facto Customary Government.
Asali: Legit.ng