Kwankwaso ya soki yunkurin gwamnatin Ganduje na ciyo bashin N20bn domin gina gada a Kano
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya soki yunkurin gwamnatin Abdullahi Ganduje na Kano game da ciyo bashin naira biliyan 20 domin gina gada a birnin jihar
- Kwankwaso ya bayyana cewa al'umman jihar Kano sun fi bukatar ilimi fiye da aikin gina gada
- Tsohon gwamnan na jihar Kano ya kuma bayyana cewa aikin gina gadar na gwamnatin tarayya ne domin a lokacinsu da kudin gwamnatin waccan lokacin suka gina tasu
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki magajinsa, Abdullahi Umar Ganduje game da shirin da gwamnatinsa ke yi na ciyo bashin naira biliyan 20 domin aiwatar da aikin gina gada a birnin jihar.
A cewar Kwankwaso, hakan ba daidai bane ga gwamnati ta ciyo bashin da zai bar al’ummar da za a haifo nan gaba da gwagwarmayar biyan bashi.
A wata hira da yayi da sashin BBC, tsohon gwamnan ya ce gina gadar wadda ta hada birnin Kano da hanyar zuwa Wudil, hakki ne da ya rataya a kan wuyar gwamnatin tarayya.
KU KARANTA KUMA: Dalla-dalla: Hanyoyin da za ka bi don yin rijistar jarabawar UTME na 2021
Ya ce:
"Maimakon a ce gwamna ya je ya ga Buhari domin ya fada masa cewa ‘ka zo ka yi mana gada’, bai yi ba, gadojin da muka yi a Kano gaba dayansu da kudin gwamnatin wannan lokaci muka yi su.”
Kwankwaso ya kara da cewa duk da ana bukatar gada a Kano, amma abin da mutanen jihar suka fi bukata shi ne ilimi .
"A koya wa yayan talakawa sana'oi na hannu wanda yara za su iya rike kansu", in ji shi.
Har la yau, ya soki yadda gwamna Ganduje yake sayar da filaye lamarin da ya haddasa cece-kuce a baya-bayan nan.
Da yake magana kan makomar filayen da gwamnatin Kano ke sayarwa kuwa, Kwankwaso ya bayyana cewa matukar mulki ya koma hannunsu, toh ba makawa sai an rushe gine-ginen da aka aza kan filayen.
KU KARANTA KUMA: Akwai kura bayan NNPC ya ce za a koma saida litar man fetur a kan N234 a gidajen mai
Ya ce:
"Duk wani gurin hukuma, mutum ko ya yi bene hawa dubu a ruguzo shi, a share gurin a mayar da shi yadda yake da.”
A wani labarin, darakta janar na hukumar Zakkah da Hisbah na jihar Kano, Safiyanu Abubakar, yace ana shirin mayar da biyan Zakka ya zama wajibi ga dukkan 'yan siyasa kafin su tsaya takara a jihar.
Abubakar ya sanar da hakan a ranar Alhamis a ofishinsa yayin rantsar da kwamitin mutum 11 na karbar Zakka a jihar.
Kamar yadda yace, wannan al'amarin ana son tabbatar dashi ne domin taimakon mabukata a jihar.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng