Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sabunta Naɗin Shugaban Hukumar BPE

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sabunta Naɗin Shugaban Hukumar BPE

- Shugaban kasa Muhammadu ya amince da sabunta nadin Alex Okoh, shugaban BPE

- Sanarwar sabunta nadin ta fito ne daga bakin babban hadimin shugaban kasa a fanin kafafen watsa labarai, Laolu Akande

- Sabunta nadin da aka yi wa Mr Alex Okoh za ta fara aiki ne daga ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2021

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sabunta nadin Mr Alexander Ayoola Okoh a matsayin shugaban hukumar sayar da hannun jari, BPE, karo na biyu na tsawon wa'addin shekaru hudu, Vanguard ta ruwaito.

Sanarwar sabunta nadin ta fito ne daga bakin babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafafen watsa labarai, ofishin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande.

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sabunta Nadin Shugaban Hukumar BPE
Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sabunta Nadin Shugaban Hukumar BPE. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: 'Yan Hisbah Sun Kai Sumame Gidan Ɗaliban Jami'a, Sun Kama Mace da Namiji a Ɗaki Ɗaya

Akande ya yi bayanin cewa nadin ya yi dai-dai ta sashi na 17 (1) (a) da (2)(a) na Public Enterprise (Privatization & Commercialization) Act, 1999.

Sabunta nadin zai fara aiki daga ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2021 a cewar sanarwar.

KU KARANTA: Kano: Hisbah za ta ci ɗaliban jami'a mace da namiji da aka kama a ɗaki ɗaya tarar N20,000 kowannensu

Hukumar BPE ma'aikata ce ta gwamnatin tarayya da ke kula da sauya-sauye na tattalin arziki musamman sayar da kadarori/kamfanonin gwamnati ga yan kasuwa da za su inganta su.

BPE kuma ita ce sakatariyar Cibiyar Sayar da Kadarori/Kamfanonin gwamnati na kasa.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel